Dino Melaye ya fadi dalilin da yasa ba zai mika kansa ga 'yan sanda ba

Dino Melaye ya fadi dalilin da yasa ba zai mika kansa ga 'yan sanda ba

- Dino Melaye ya yi ikirarin cewa Sufeta Janar na 'yan sanda yana shirin kashe shi hakan yasa yaki mika kansa ga 'yan sanda

- Sanatan mai wakiltan mazaban Kogi ta yamma ya ce ba tsoro ne yasa ya boye ba sai dai hikima makamancin wadda Annabi Elijah ya yi a cikin Bible

- A bangarensu, 'yan sanda sun ce ana zargin Dino Melaye ne da hannu cikin aikata fashi da makami tare da shirya kisan kai

Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi ta yamma da ke cigaba da buya ya fadi dalilin da yasa ba zai mika kansa ga hukumar 'yan sandan Najeriya ba.

Mr Melaye ya yi ikirarin cewa Sufeta Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris yana son yasa ayi masa allurar guba da zata kashe shi muddin ya mika kansa ga 'yan sandan hakan yasa ya cigaba da buya.

Sanatan ya kwatanta halin da ya shiga a yanzu da gwagwarmayar da Annabi Elijah ya yi a littafin Bible mai tsarki a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren ranar Talata.

Dino Melaye ya fadi dalilin da yasa ba zai mika kansa ga 'yan sanda ba

Dino Melaye ya fadi dalilin da yasa ba zai mika kansa ga 'yan sanda ba
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

Premium Times ta ruwaito a baya yadda 'yan sandan suka mamaye gidan Dino Melaye da ke Abuja a ranar Juma'a inda suka ce ana tuhumarsa da hannu cikin fashi da makami da shirya kisan kai.

Wannan dai shine karo na hudu da jami'an yan sanda su kayi yunkurin kama Dino Melaye a cikin shekarar 2018 da ta gabata.

A sakon da mai magana da yawun 'yan sanda Jimoh Moshood ya fitar, ya ce Dino Melaye tare da 'yan dabarsa sun harbi wani jami'in dan sanda mai mukamamin Saja, Danjuma Saliu a watan Yulin 2018.

A maimakon ya karyata zargin da 'yan sanda ke masa, Dino Melaye kawai ya ce hikima ce ta sa ya cigaba da kasancewa a inda ya ke buya amma ba tsoro ba.

Melaye ya ce Annabi Elijah yana daya daga cikin Annabawa masu karfi a cikin Bible amma ya tafi Dutsen Carmel ya buya a lokacin da Sarki Ahab ke nemansa domin ya kashe shi saboda ya fadi gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel