Dalibai zasu koma karatu: Gwamnatin tarayya ta sakarwa ASUU N15.89bn

Dalibai zasu koma karatu: Gwamnatin tarayya ta sakarwa ASUU N15.89bn

- Gwamnatin tarayya ta dauki matakin kawo karshen yajin aikin da kungiyar ASUU ta shiga tun shekarar data gabata

- Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin ta sakarwa ASUU N15.89bn, wanda ake hasashen zasu shiga asusun jami'o'in a ranar Laraba

- Sai dai shugaban ASUU na shiyyar Kudu maso Yamma, Dr. Deji Omole ya ki tsokaci kan wannan labari na cewar kungiyar ta cimma matsaa da gwamnatin tarayya

Da alamun cewa jami'o'in Nigeria na daf da dawowa bakin aiki nan ba da jimawa ba, a yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i suke kan gudanarwa.

Gwamnatin tarayyar zata tabbatar da wannan yunkurin nata kafin ranar Litinin, inda shuwagabannin kungiyar ASUU da ministan kwadago da dauki aiki, Chris Ngige zasu hadu. Ministan dai na kan fafutukar ganin ya lallashi shuwagabannin ASUU akan janye yajin aikin, ta hanyar cika masu burukan nasu.

A ranar 4 ga watan Nuwambar shekarar data gabata, malaman jami'o'i suka fada yajin aikin fadin kasar sakamakon gazawar gwamnatin tarayya na cimma yarjejeniyar 2017. Yarjejeniyar dai ta biyo baya bin diddigin alkawarin da gwamnatin tarayyar ta daukarwa kungiyar a shekarar 2009, tun a mulkin marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa 'Yar Adua.

KARANTA WANNAN: Idan kuna son ci gaban Nigeria a 2019, ku zabi Buhari - Obaseki

Dalibai zasu koma karatu: Gwamnatin tarayya zata sakarwa ASUU N15.89bn

Dalibai zasu koma karatu: Gwamnatin tarayya zata sakarwa ASUU N15.89bn
Source: UGC

Shugaban ASUU na kasa Biodun Ogunyemi ya alakanta wannan yajin aikin da gazawar gwamnatin na cimma bukatunsu da kuma cika alkawarin da ta daukarwa kungiyar.

Sai dai a ranar Litinin, gwamnatin tarayyar tayi kokarin shawo kan wannan matsalar da kuma tabbatar da kudurinta na cimma bukatun malaman da kungiyoyinsu.

"Daya daga cikin sharadin da aka cimmawa shine, gwamnatin tarayya zata sakarwa jami'o'in N15.89bn a ranar Litinin, ana sa ran kudaden zasu shiga asusun jami'o'in a ranar Laraba," a cewar wata majiya.

Sai dai shugaban ASUU na shiyyar Kudu maso Yamma, Dr. Deji Omole ya ki tsokaci kan wannan labari na cewar kungiyar ta cimma matsaa da gwamnatin tarayya. Omole, wanda shine shugaban ASUU reshen jami'ar Ibadan ya ce har yanzu gwamnatin bata kira wani taro don kawo karshen yajin aikin ba tsawon makonni 2 da suka gabata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel