PDP na bayar da gudunmuwa ta rashin tsaro a Najeriya - APC

PDP na bayar da gudunmuwa ta rashin tsaro a Najeriya - APC

Jam'iyya mai ci ta APC na ci gaba da zargin jam'iyyar adawa ta PDP da dukkanin makarrabanta wadanda ke da kusanci da gwamnatin da kuma sabanin haka wajen bayar gudunmuwa ta haddasa rashin tsaro a Najeriya da kuma yada ƙarairayi.

APC ta ce akwai kitimurmura da jam'iyyar adawa ta PDP ke faman kullawa domin tayar da zaune tsaye cikin kasar nan makamancin yadda ta yi a tsakanin shekarar 2014 da kuma 2015 da suka gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ta dasa 'yan ta'adda a lokutan baya inda suka ci karen su ba bu babbaka cikin wasu sassa na kasar nan kamar yadda jam'iyyar APC ta zayyana.

PDP na bayar da gudunmuwa ta rashin tsaro a Najeriya - APC

PDP na bayar da gudunmuwa ta rashin tsaro a Najeriya - APC
Source: Twitter

A yayin haka jam'iyyar APC ta ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba za ta taba saduda ba dangane da wannan mummunar ta'ada da tsagwaran adawa, inda ta ke kira ga al'ummar kasa akan juya baya ga jam'iyyar PDP yayin babban zaben kasa da za a gudanar a watan gobe.

Mallam Lanre Issa-Onilu, babban sakataren hulda da al'umma na jam'iyyar APC, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a jiya Talata cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa za ta kashe N274m akan wutar lantarki, N65m akan dabbobin kiwo

Issa-Onilu ya kuma ce dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba ya da wasu nagartattun tsare-tsare domin samar da kyakkyawar makoma ta fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira.

Ya kuma zayyana yadda tsohon mataimakin shugaban kasar ya durkusar da ci gaban Najeriya yayin da ya jagoranci kwamitin sayar da kamfanin wutar lantarki na kasa a lokacin gwamnatin su ta tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel