Muna fama da barazana a jahar Borno – Inji Gwamna Kashin Shettima

Muna fama da barazana a jahar Borno – Inji Gwamna Kashin Shettima

Gwamnan jahar Borno, Kashim Shettima ya bayyana cewa akwai manyan manyan kalubale dake fuskantar jahar Borno, musamman duba da yadda ayyukan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ke kara ruruwa a jahar.

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Litinin data gabata yayin wani taron gaggawa na musamman da aka shirya aMaiduguri wanda ya samu halartar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da suka hada da shuwagabannin Sojoji, DSS, Yansanda da sauransu.

KU KARANTA; Kungiyar Musulman Najeriya ta koka kan kashe kashen da ake yi a Zamfara

Gwamnan yace ya kira taron ne domin tattauna matsalolin da ake fama dasu a yaki da ta’addanci a jahar Borno, tare da lalubo hanyoyi ko matakan magance wadannan matsaloli, gwamnan ya cigaba da fadin cewa za’a iya samun nasara ne kawai idan sun yi aiki a matsayin tsintsiya madaurinki daya.

Muna fama da barazana a jahar Borno – Inji Gwamna Kashin Shettima

Gwamna Kashin Shettima
Source: Facebook

“A yau muna fama da kalubale da dama a jahar Borno, amma ina fatan kalubalen nan zasu kara mana kwarin gwiwa don ganin mun taimaka ma rundunar Sojojin Najeriya, Yansanda, DSS, da kuma Sojojin sa kai don ganin an kawo karshen Boko Haram.

“Dukkanmu muna da rawar daya kamata mu taka wajen cimma manufarmu, don haka yasa na yi taka tsantsan wajen zabo mahalarta wannan taro, ba wai mun taru nan bane don bayyana wanene mai laifi ko kuwa, domin a ganina bamu Sojoji adalci ba idan muka taru ana muka zargesu ba.” Inji shi.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Gwamna Kashim ya jinjina ma kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi game da matsalar Boko Haram, inda yace ya tabbata Buhari nada niyya, duba da yadda yake hada kan kashen dake makwabtaka da Najeriya wajen yaki da Boko Haram.

Idan za’a tuna, ayyukan kungiyar Boko Haram sun yi Kamari a yan kwanakin baya, inda mayakan kungiyar suka kai munanan hare hare a kauyukan jahar Borno da Yobe, tare da kai hare haren kunar bakin wake, haka zalika kungiyar ta kasha Sojojin Najeriya da dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel