Buhari ya kafa tubali na ci gaba a Najeriya - Tinubu

Buhari ya kafa tubali na ci gaba a Najeriya - Tinubu

- Babban jigo na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya kira kan zaben shugaba Buhari a zaben watan gobe

- Ya ce zaben shugaba Buhari da jam'iyyar APC ita kadai ce hanyar tsira a yanzu

- Tinubu ya ce shugaba Buhari ya kafa wani tubali na cigaban kasa domin fidda A'i daga Rogo

Babban jagora kuma kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyya mai ci ta APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya kirayi 'yan Najeriya akan su fito kwansu da kwarkwata wajen dangwalawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri'un su a zaben kasa da za a gudanar a watan Fabrairu na gobe.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, domin ramawa Kura kyakkyawar aniyyarta, babban jagoran na jam'iyya mai ci ya nemi daukacin al'ummar Najeriya akan zaben shugaba Buhari sakamakon nasarorin da ya yi bisa kujerar mulki tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Buhari ya kafa tubali na ci gaba a Najeriya - Tinubu

Buhari ya kafa tubali na ci gaba a Najeriya - Tinubu
Source: UGC

Tinubu ya ke cewa, baya ga kwazon da kuma nagartacciyar bajinta akan habaka da kuma inganta harkokin noma, shugaban kasa Buhari ya kuma dasa wani tafarki gami da kafa kyakkyawan tubali na ci gaban kasa domin fidda A'i da Rogo.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa, zaben shugaban kasa Buhari da kuma jam'iyyar sa ta APC su na kafada da juna wajen fidda kasar nan zuwa ga Tudun tsira mai hasken gaske da ya kasance dalili daya tilo da rage ga al'ummar kasar nan.

KARANTA KUMA: Dalilai 9 da suka haddasa talauci a Arewacin Najeriya - Shehu Sani

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin zayyana sakonnin sa na taya murnar sabuwar shekara, inda ya nemi al'ummar Najeriya akan sauke nauyin da rataya a wuyan su na zaben nagartattun jagorori masu kishin kasa.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar Kiristoci reshen Arewacin Najeriya, ta yi kira akan kada a sake zabi shugaban kasa Buhari yayin babban zaben kasa da zai gudana a watan gobe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel