An zargi 'yan siyasar Borno da rura wutar fargaba kan Boko Haram

An zargi 'yan siyasar Borno da rura wutar fargaba kan Boko Haram

- An zargi yan siyasa a jihar Borno dangane da hargitsin da yake faruwa a yankin

- Wasu daga cikin yan siyasar suna amfani da damar rashin kwanciyar hankalin jihar su azurta kansu

- Ba zamu kara bari yan siyasa suyi wasa da rayukan mu ba

An zargi 'yan siyasar Borno da rura wutar fargaba kan Boko Haram

An zargi 'yan siyasar Borno da rura wutar fargaba kan Boko Haram
Source: UGC

Rahoto ya bayyana cewa ana zargin yan siyasa a jihar Borno da taimakawa wajen hargitsin dake faruwa a yankin.

Wannan batu ya fito ne daga bakin Arewa Youth integrity forum( AYIF) wanda suka fitar a ranar Lahadi.

Kungiyar ta bayyana damuwar ta akan halin da kasar take ciki a bangaren tsaro musamman a bangaren yan siyasar jihar Borno.

AYIF sunce wasu daga cikin yan siyasa suna amfani da halin da jihar ta Borno ke ciki suna azurta kawunan su.

DUBA WANNAN: Illoli da alfanun shan maganin takaita haihuwa da kiyayyar daukar ciki

Alhaji Sani Kolo sakatare janar na kungiyar yace wasu yan siyasa suna bada goyan baya akan hare hare da ake kaiwa jihar ta Borno.

Kolo ya kara da cewa "Muna da rubutattun saqonnin waya da mutanen mu wadanda suke mazauna Bama, Dikwa da Munguno suka turo mana, saqonnin sun fito daga wajen wadanda suke makusantan su."

Abu ne da ya bayyana cewa wadannan matsaloli da ake fama dasu akwai daurin gindin yan siyasa a ciki saboda basa bukatar ganin kawo karshen ta'addanci a Najeriya.

Mun yanke hukuncin cewa bazamu kara yadda ayi wasa da rayukan mu ba dan biyan bukatar su.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel