Sabuwar shekara ta 2019 dama ce ga jagorori da mabiya su kyautata rayuwar su - Jonathan

Sabuwar shekara ta 2019 dama ce ga jagorori da mabiya su kyautata rayuwar su - Jonathan

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya taya al'ummar Najeriya murnar sabuwar shekara ta 2019

- Goodluck ya ce sabuwar shekarar nan ta na kunshe da alherai domin al'ummar Najeriya su ribatu

- Ya yi kira kan kyautata rayuwa da kuma inganta mu'amala a tsakanin jagorori da kuma mabiya

Tsohon shugaban kasa na Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, cikin sakon sa na taya murnar sabuwar shekara, ya ce shekarar 2019 wata gagarumar dama ce ga 'yan Najeriya domin su inganta rayuwar su gami da kyautata zamantakewar su.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa, wannan sabuwar shekara wata babbar dama ce musamman ga shugabanni da kuma mabiya domin kyautata rayuwar su da kuma ma'amala.

Cikin sakon sa na taya murnar sabuwar shekara da ya rubuta a shafin sa na sada zumunta na Twitter, tsohon shugaban kasar ya kyautata zato gami da kyakkyawan fata na bunkasar Najeriya da kuma kai wa zuwa ga tudun tsira.

Sabuwar shekara ta 2019 dama ce ga jagorori da mabiya su kyautata rayuwar su - Jonathan

Sabuwar shekara ta 2019 dama ce ga jagorori da mabiya su kyautata rayuwar su - Jonathan
Source: Depositphotos

Ya ke cewa tabbas sabuwar shekara ta 2019 wata babbar dama ce ga jagorori da kuma mabiya domin kyautata rayuwarsu da kuma zamantakewa domin ribatuwa da wannan romo da kuma cin gajiyar hakan a gobe.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya kan hada kawunan su wuri guda ba tare da nuna bambanci na addini ko kuma kabilanci da ya kasance daya daga cikin muhimman kudurori na magabatan kwarai.

KARANTA KUMA: Rayukan Mutane 30 sun salwanta yayin bikin sabuwar shekara a garin Ibadan

Jonathan ya na kuma taya dukkanin al'ummar kasa baki daya murnar wannan sabuwar shekara ta 2019 da ya kyautata mata zato gami da kyakkyawan fata.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kungiyar Kiristocin Arewa sun yi kira ga 'yan Najeriya akan kada su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin babban zaben kasa da za gudanar a watan Fabrairu na gobe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel