Dokar hana kiwo: Gwamnati ta mayar da shanu 187 da ta kwace ga makiyaya a Benuwe

Dokar hana kiwo: Gwamnati ta mayar da shanu 187 da ta kwace ga makiyaya a Benuwe

Gwamnatin jahar Benuwe ta saki wasu shanu guda dari da tamanin da bakwai (187) da jami’an hukumar hana kiwon shanu a garin Makurdi suka kama tare da kwace daga hannun yan Fulani makiyaya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito a ranar Talata 1 ga watan Janairu ne hukumar ta mika dabbobin ga masusu, tare da gargadin kada su kuskukura ta sake kama dabbobin nasu, sai dai wannan lamari ya faru ne bayan kwanaki biyu da hukumar ta sako wasu shanu guda dari da biyar da suma ta kamasu suna kiwo a Makurdi.

KU KARANTA: Kalli mutumin da Gwamna Tambuwal ya nada sabon Alkalin Alkalan jahar Sakkwato

Dokar hana kiwo: Gwamnati ta mayar da shanu 187 da ta kwace ga makiyaya a Benuwe

Shanu
Source: UGC

Kwamishinan noma na jahar Benuwe, Hyacinth Nyakuma ne ya sanar da haka a yayin da yake mika shanu 187 ga masu su a garin Makurdi, inda yace har yanzu dokar hana kiwon dabbobi a Makurdi na aiki, don haka yayi kira ga shuwagabannin Fulani dasu ilimantar da jama’ansu game da dokar.

“Alamu sun nuna makiyaya basu da niyyar yi ma wannan doka biyayya, domin kuwa bamu dade da sakin rukunin farko na shanun da muka fara kamawa ba, sai ga shi mun sake kama wasu shanun.

“Jahar Benuwe bata kafa wannan hukuma don tattara kudade ba, a’a, manufar dokar da kuma hukumar shine tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar dake zaune a garin Makurdi da ma jahar Benuwe gaba daya” Inji shi.

Da wannan ne kwamishina Nyakuma yayi kira ga dukkanin hukumomin tsaro dake jahar dasu dabbaka wannan doka a duk inda suke domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jahar, haka zalika yace ana ciyar da dabbobin da aka kama tare da basu magani.

Shima a nasa jawabin a yayin karbar dabbobin, shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jahar Benuwe, Ubi Haruna ya bayyana godiyarsa da sassaucin da gwamnatin jahar Benuwe ta nuna wajen sakin wadannan dabbobi da suka hada da shanu 187 da tumaki 44.

Daga karshe yayi alkawarin kungiyarsu zata ilimantar da yayanta game da dokar, sa’annan ya nemi gwamnatin ta kara musu lokaci don cimma sharudda da duk wasu bukatun da dokar ta nema.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel