Idan kuna son ci gaban Nigeria a 2019, ku zabi Buhari - Obaseki

Idan kuna son ci gaban Nigeria a 2019, ku zabi Buhari - Obaseki

- Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi kira ga 'yan Nigeria da su sake baiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari dama a karo na biyu

- Obaseki ya ce sake zabar APC a 2019 zai baiwa shugaban kasa Buhari damar ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba da ya fara shimfidawa a kasar

- Obaseki ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen daga darajar Ilimi, kiwon lafiya daga matakin farko da kuma noma

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi kira ga 'yan Nigeria da su tabbatar da dorewar ayyukan raya kasa da ci gaban al'umma da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samar a cikin shekaru hudu, ta hanyar sake zabar APC a 2019.

Mr. Godwin Obaseki ya yi wannan kiran a wajen gabatar da ibadu a babbar cocin Cathedral ta St. John, da ke karamar hukumar Owan ta Yamma, a ranar Talata.

Gwamnan ya ce idan har jama'ar Nigeria suka kad'a kuri'arsu ga jam'iyyar APC a zabukan 2019 da ke gabatowa, zai baiwa shugaban kasa Buhari damar ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba da ya fara shimfidawa a kasar.

KARANTA WANNAN: Asiri ya tonu: Yadda APC ta shirya tafka uban magudi a jihar Buhari - PDP

Gwamna Godwin Obaseki

Gwamna Godwin Obaseki
Source: Depositphotos

"Muna sane da cewa Nigeria na fuskantar tulin matsaloli, amma kowa ya gani, gwamnatinmu ta yi bakin fama wajen kawo ci gaba a cikin shekaru hudu. Dole mu tabbatar da dorewar wadannan ayyuka da muka fara ta hanyar zabar APC a karo na biyu."

Gwamnan ya ce hauhawar adadin 'yan Nigeria abun tsoro ne, musamman duba da halin da kasar take ciki. Sai dai ya ce shugaban kasa Buhari na iya bakin kokarinsa na ganin ya dai-daita hakan ta hanyar samar da ayyukanyi, bunkasa rayuwar jama'a da kuma samar da hanyoyin gudanar da rayuwa cikin sauki.

Obaseki ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen daga darajar Ilimi, kiwon lafiya daga matakin farko da kuma noma don jawo masu saka hannun jari a masana'antu a jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu. L

atsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel