Asiri ya tonu: Yadda APC ta shirya tafka uban magudi a jihar Buhari - PDP

Asiri ya tonu: Yadda APC ta shirya tafka uban magudi a jihar Buhari - PDP

- Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta ce ta gano shirn jam'iyyar APC na tafla magudi a zaben 2019

- Shugaban jam'iyyar na jihar, Salisu Majigiri, ya ce kudurin APC na hadawa Buhari kashi 100 na kuri'un Katsina alama ce karara ta shirin tafka magudi

- Haka zalika PDP a jihar ta kaddamar da sabon shiri mai taken 'PDP Sawuta' da nufin zakulo magoya bayan jam'iyyar daga matakin farko

Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta ce bayyana aniyar shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, na samawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kashi 100 na kuri'un da za a kad'a a jihar Katsina, babbar alama ce ta cewar gwamnan jihar Aminu Masari da APC na shirin tafka uban magudi a zaben 2019.

Shugaban jam'iyyar, Salisu Majigiri ya sanar da Daily Trust cewar fargar yin magudi a zaben, ya tabbata gaskiya ne tun bayan da Oshiomhole ya sanar da wannan yunkuri nasu.

A cewarsa, dukkanin wasu hanyoyin da aka yi amfani da su don kayar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben 2014, Goodluck Jonathan, a yanzu sun kau, yana mai cewa, "Ina mamakin hanyar da zasu bi har su samu kashi 100 na kuri'un jihar.

KARANTA WANNAN: Na tuka motar dana kera daga Legas zuwa Abuja domin in hadu da Buhari - Obasanjo

Asiri ya tonu: Yadda APC ta shirya tafka uban magudi a jihar Buhari - PDP

Asiri ya tonu: Yadda APC ta shirya tafka uban magudi a jihar Buhari - PDP
Source: Facebook

"A shekarar 2015, APC ta yi amfani da aringizon kuri'u da kuma bijiro da kabilaci ga dan takarar shugaban kasa na wancan lokacin, amma duk da hakan PDP ta samu kuri'u 10,000 a jihar Katsina, don haka a yanzu da babu wadancan dabarun, babu ta yadda APC zata iya kayar da mu," a cewarsa.

Ya ce, a halin matsin rayuwa da gwamnatin APC ta jefa kasar a ciki, kan jama'ar kasar ta waye kuma kowannensu na son canja canjin da ya gaza cika masu alkawuran da aka daukar masu tsawon shekaru uku da rabi na gwamnatin canjin.

A wani labarin makamancin wannan, jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta kaddamar da wani sabon shiri mai taken "PDP Sawuta", wanda aka samar da shi da nufin zakulo magoya bayan jam'iyyar tun daga matakin farko, don fuskantar babban zaben 2019.

Shugaban jam'iyyar, a bukin kaddamar da shirin, ya bayyana cewa shirin idan har ya kankama zai taimakawa jam'iyyar wajen samun gagarumar nasara a zaben 2019 a jihar.

A jawabinsa, shugaban shirin, Gambo Mai-Walda, ya ce kudurin shirin shine samun mutane 25,000 da zasu bada gudunmowarsu wajen jan ra'ayoyin mutane 500,000 domin zabar jam'iyyar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel