Rayukan Mutane 30 sun salwanta yayin bikin sabuwar shekara a garin Ibadan

Rayukan Mutane 30 sun salwanta yayin bikin sabuwar shekara a garin Ibadan

Da ya ke dai Hausawa na cewa mai rabon ganin badi ko ana daka sa cikin Turmi sai ya gani, mun samu cewa hakan ba ta kasance ga wasu Mutane 30 ba da ajali ya katse ma su hanzari ana daf da afkawa sabuwar shekara ta 2019.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, rayukan wasu Mutane 30 sun salwanta cikin abun da bai wuci gabanin dakikai 15 da afkawa cikin wannan sabuwar shekara ta 2019 a daren ranar Litinin din da ta gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, rayukan wannan adadi na mutane sun salwanta a sakamakon wani mummunan hatsarin Mota da ya auku daura da babbar kasuwar Bola Ige ta kasa da kasa da ke kan hanyar Ife ta garin Gbagi na birnin Ibadan a jihar Oyo.

Rayukan Mutane 30 sun salwanta yayin bikin sabuwar shekara a garin Ibadan

Rayukan Mutane 30 sun salwanta yayin bikin sabuwar shekara a garin Ibadan
Source: Depositphotos

Manema labarai sun ruwaito cewa, hatsarin ya auku ne yayin da wata babbar Mota kirar Tirela ta murkushe Mutane 30 nan take yayin da ta shararo hanya daga garin Iwo kuma ta afka kan wasu Motocin haya da ke iyaka ta mashigar kasuwar Bola Ige.

Wannan mummunan hatsari da ya auku da misalin karfe 11.45 na Yammaci ya janyo tsaiko da ya yi sanadiyar jerin gwanon Motoci tare da jefa matafiya cikin halin kaka-nika-yi na tsawon sa'o'i da dama.

KARANTA KUMA: Rayuka 8 sun salwanta, Mutane 9 sun jikkata yayi wasu hare-hare cikin jihohin Filato da Kaduna

Kazalika manema labarai sun yi shaidar wata annobar Gobara da 'yan kwana-kwana su ka yaka yayin da ta lashe dukiya mai tarin yawa a wani katafaren shago da ke daura da filin wasanni na Lekas Salami a birnin Ibadan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki a wata katafariyar gonar shinkafa mallakin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, inda suka kone ta kurmus.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel