Ta'aziyyar da Jonathan ya kai Sokoto: Bayanan Peter Obi ga jama'ar Sokoto masu sosa rai

Ta'aziyyar da Jonathan ya kai Sokoto: Bayanan Peter Obi ga jama'ar Sokoto masu sosa rai

- Jonathan dai ya riga shugaba Buhari isa Sokoto jana'iza

- Peter Obi mai neman kujerar Osinbajo yayi bayanai masu sosa rai

- Yace akwai darussa sosai da za'a koya daga rayuwar Shagari

Ta'aziyyar da Jonathan ya kai Sokoto: Bayanan Peter Obi ga jama'ar Sokoto masu sosa rai

Ta'aziyyar da Jonathan ya kai Sokoto: Bayanan Peter Obi ga jama'ar Sokoto masu sosa rai
Source: Twitter

A ziyarar da suka yi maza suka riga shugaba Buhari halarta, ta jana'izar tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari, shugaba Jonathan da mai takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Peter Obi, sun yaba da rayuwar dattijon.

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Mista Peter Obi ya kwatanta mutuwar tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari a matsayin babban rashi mai dauke da darasi da kalubale ga Najy. Obi ya fadi hakan ne a jiya da ya raka tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sakwato gurin ta'aziyyar marigayin ga iyalan shi, gwamna Tambuwal da kuma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar.

A yayin yake amsa tambayar manema labarai, Obi yace idan aka dubi mulkin Shagari za'a iya hango boyayyun darussa.

A kalaman Obi: "Bayan kuma darussa a kishin kasa da aiki tukuru, Shagari ya nuna cewa kan kan da kai,damuwa da soyayya su zamo jigon shugabanci, wadanda sune jigon shugabancin Atiku."

Obi ya kwatanta Shagari da "Wayayye, mai juriyayda kuma goggagen da siyasa kuma shugaba abin duba da kwaikwayo ga kowa," yace daga cikin shirye shiryen da ya kirkiro yayin mulkin kasar sun hada da "Green Revolution"

Akan kalubalen rasuwar Shagari, Obi yace ire iren su Shagari na ta karewa kuma hakan kalubale ne ga matasa wajen rungumar kujerun mulki.

Ya jadadda cewa shugabancin kasar da Atiku zai yi kadai zai gano hakan da kyau, Obi yace masu taya Atiku mulki zasu kasance kashi 40 mata da matasa in har aka zabe shi.

Da ya tuna da dangantakar tsohon shugaban kasar da mataimakin shi na lokacin, Dr Alex Ekwueme. Obi yace a 2019 zai zama shekaru 40 cif kenan rabon da dan kudu maso gabas ya shiga shugabancin kasa, wanda yan yankin zasu zamo masu godiya gareshi har abada.

Cewarsa, Peter Obi, rayuwar Shehu Shagari tana da darussa sosai da za'a iya koya ko bayan rasuwarsa, inda ya kira Shagari da cewa dattijo ne mai yafiya da dattako, da rikon addini da son kowa, da ma kyautayi.

DUBA WANNAN: Ajandar Boko Haram: Ashe wai suna so su kwaci Damasak, Monguno da Abadam cikin makonnin nan ne

Peter Obi, ya kuma ce, irin rayuwar Shagari, sak take da irin ta Atiku Abubakar, wanda ya maida kowa nasa a fadin kasar nan, ba tare da tsangwama ko hantara ba, inda ake ganin shagube ne yake wa gwamnatin APC da uban tafiyarta.

Shi dai shugaba Buhari a 1983, shine ya tumbuke gwamnatin Shagarin, inda yace duk su barayi ne, sun wawure dukiyar jama'a a shekaru hudu, ya kuma kulle shugaban kasar shekaru har biyu a kurkuku.

A lokacin na, tsabar yada jita-jita, akan ce ai Ummaru Dikko ya kwashe gaba dayan kasafin kudin kasar nan ne na shekara guda, ya gudu dasu Ingila, lamari da yasa Buharin ya sa aka sato masa shi a akwati tun daga Ingila don fuskantar tuhuma, amma ta tashi.

Allah dai Ya ji qan Shagari mazan jiya, ya yafi kura-kurai nai...

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel