Rayuka 8 sun salwanta, Mutane 9 sun jikkata yayin wasu hare-hare cikin jihohin Filato da Kaduna

Rayuka 8 sun salwanta, Mutane 9 sun jikkata yayin wasu hare-hare cikin jihohin Filato da Kaduna

Da ya ke dai rahotanni dangane da aukuwar hare-hare a fadin kasar nan ba sabon lamari ba ne musamman cikin 'yan shekaru kadan da suka gabata, mun samu cewa wani harin masu tayar da zaune tsaye yayi muni cikin jihohin Kaduna da Filato.

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu cewa, rayukan Mutane 8 sun salwanta tare a jikkatar Mutane 9 a ranar Lahadin da ta gabata yayin da wasu bindiga suka zartar da hare-hare kashi-kashi a jihar Kaduna da kuma Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa, rayukan mutane hudu sun salwanta yayin aukuwar wani mummunan hari a kauyen Ndinng da ke karkashin karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato, inda mutane biyu kuma suka jikkata.

Rayuka 8 sun salwanta, Mutane 9 sun jikkata yayi wasu hare-hare cikin jihohin Filato da Kaduna

Rayuka 8 sun salwanta, Mutane 9 sun jikkata yayi wasu hare-hare cikin jihohin Filato da Kaduna
Source: Facebook

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Terna Tyopev, shine ya bayar da shaidar wannan lamari yayin ganawa da manema labarai kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Kazalika a ranar Lahadin da ta gabata, wasu maharan rike da makamai na bindigu sun zartar da wani hari na daban a kauyen Katuru da ke karkashin karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, inda rayukan mutane hudu suka salwanta.

Ko shakka ba bu ana zargin makiyaya da zartar da wannan hare-hare sakamakon wasu sakonni da suka aike da su na barazana da kuma gargadin kai hari a yankunan.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya za su ribatu da albarkar shekarar 2019 - Okorocha

A yayin da manema labarai suka yi yunkurin tabbatar da sahihancin wannan rahoto, hakar su ba ta cimma ruwa ba, inda jagoran wata kungiya ta Adara Development Association, Mista Awema Dio Maisamari, ya bayar tabbacin wannan lamari.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hare-haren sun auku duk da jami'an tsaro da hukumar 'yan sanda da watsa domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel