Da dumi dumi: Yan bindiga sun aikata ma wani gwamnan Arewa danyen aiki a gonarsa

Da dumi dumi: Yan bindiga sun aikata ma wani gwamnan Arewa danyen aiki a gonarsa

Wasu gungun yan bindiga sun kai farmaki zuwa wata katafariyar gonar shinkafa mai mallakin gwamnan jahar Benuwe, Gwamna Samuel Ortom, inda suka banka mata wuta tare da konata kurmus, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.com ta ruwaito ita dai wannan gona mai girman ekta 250 tana kauyensu gwamnan ne, watau kauyen Gbajimba dake cikin karamar hukumar Guma na jahar Benuwe.

KU KARANTA: Duniya mai yayi: Alkalin Alkalai na jahar Sakkwato ya yi murabus

Da dumi dumi: Yan bindiga sun aikata ma wani gwamnan Arewa danyen aiki a gonarsa

Gwamnan a gonar
Source: Facebook

Sai dai rahotanni daga majiyoyi masu suka sun tabbatar da cewar Gwamna Samuel Ortom ya tafka asarar sama da naira miliyan dari (N100,000,000) a wannan gona sakamakon wutar da yan bindigan suka banka ma wan yankinta.

A ranar Talata 1 ga watan Janairu ne manema labaru suka samu damar zagayawa cikin gonar tare da manajan gonar, Kena Iordzua, wanda ya bayyana cewa a kwanakin bayan ne yan bindigan suka dira gonar tare da garke garke na shanu.

A cewar manajan gona Kena, diran yan bindigan gonar keda wuya da tsakar rana, sai suka banka ma gona wuta a wurare guda uku sa’annan suka kara gaba, amma sakamakon lokaci ne na hunturu sai wutan ta kama ci bal bal, don haka duk kokarin da aka yi na kasheta ya ci tura.

Daga bisani an tura jami’an tsaro su bi sawun yan bindigan, a cewar manaja Kena, amma basu samu nasarar kama yan bindigan ba. Shima hadimin gwamnan akan ayyuka na musamman, Abraham Kwaghngu ya yi Allah wadai da wannan hari.

Mista Abrahm ya bayyana harin a matsayin aikin kawai, sa’annan ya kara da cewa hakan wata makarkashiyace ga samun yalwan abinci a jahar Benuwe da wasu makiya jahar suke shiryawa.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin kwamishinan Yansandan jahar, Ene Okon, game da lamarin bai yiwa ba sakamakon baya daukan wayan da aka yi masa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel