'Yan Najeriya za su ribatu da albarkar shekarar 2019 - Okorocha

'Yan Najeriya za su ribatu da albarkar shekarar 2019 - Okorocha

Gwamnan jihar Imo kuma jagoran gwamnonin jam'iyyar APC, Rochas Okorocha, a bisa ma'auna ta fahimta da kuma hasashe, ya lasawa al'ummar Najeriya gardi da ababen morewa na albarkatu da za su ribata cikin kasar nan a wannan sabuwar shekara ta 2019.

Okorocha yayin zayyana moriyar shekarar 2019 da al'ummar Najeriya za su ribata, ya kuma gargade su akan kyautata zato gami sa ran yadda shekarar za ta albarkace su da kuma kasa baki daya fiye da shekarar 2018 da ta gabace mu.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamna Rochas ya yi wannan kira cikin sakonnin su na sabuwar shekarar da ya gabatar da sanadin babban sakataren yada labarai na fadar gwamnatin sa, Mista Samuel Omwuemeodo.

'Yan Najeriya za su ribatu da albarkar shekarar 2019 - Okorocha

'Yan Najeriya za su ribatu da albarkar shekarar 2019 - Okorocha
Source: Getty Images

Gwamna Rochas ya yi karin haske gami da gargadin cewa, ba bu wata da za ta taka mizani ko wani mataki na ci gaba matukar al'ummar ta ba sa kyautata mata zato gami da sa rai na samun mafi kololuwar ci gaba.

Jagoran gwamnonin na APC ya kirayi al'ummar Najeriya dangane da yadda za su tatsi romon mai gardin gaske gami da cin riba musamman ta fuskar habakar tattalin arziki, siyasa, hadin kai da kuma ci gaba kasa baki daya.

KARANTA KUMA: 2019: Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a sake zaben sa - Ribadu

Ya kuma kirayi daukacin al'ummar Najeriya baki daya kan kwarar yabo da kuma godiya ga Mahallacin su dangane da yadda ya sa suka kasance cikin koshin lafiya a shekarar 2018, tare da rokon sa akan kyautata masu wannan shekara fiye da wadda ta gabata.

A yayin da yake bayar da tabbaci ga al'ummar jiharsa ta Imo akan yadda zai ci gaba da jajircewa bisa aiki tukuru gabanin kammaluwar wa'adin sa a kan kujerar gwamnati, ya kuma yi ikirarin cewa yana da cikakken yakini na cika duk wasu alkawurra da gwamnatin sa ta dauka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel