2019: Zaben Buhari ba zai zama alheri ba - Kiristocin Arewa

2019: Zaben Buhari ba zai zama alheri ba - Kiristocin Arewa

- Kungiyar kiristocin Arewa sunyi kira ga 'yan Najeriya kada su zabi shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019

- Kungiyar ta ce shugaba Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka wa 'yan Najeriya a yayin yakin neman zabe

- Kungiyar ta ce ba a taba samun gwamnati mai muni kamar gwamnatin Buhari ba tun kafa Najeriya tare da lissafo matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar

Kungiyar mabiya addinin kirista na Arewa 'Arewa Christians and Indigenous Pastors Association' (ACIPA) tayi kira ga 'yan Najeriya su nemi wani dan takarar shugabancin kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari saboda shi ba alheri bane ga kasar.

A sakon sabuwar shekarar da kungiyar da fitar mai dauke da sa hannun shugaban ta Rabaran Luka Shehu, kungiyar ta ce shekarun da gwamnatin Buhari ta kwashe tana mulki sune mafi muni a tarihin Najeriya.

2019: Zaben Buhari ba zai zama alheri ba - Kiristocin Arewa

2019: Zaben Buhari ba zai zama alheri ba - Kiristocin Arewa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Atiku zai lallasa Buhari a yankin Arewa maso yamma - Kungiya

Sanarwar ta ce: "A yayin da muke sa ran samun cigaba da tsaro a Najeriya a shekarar 2019 da shekarun da za su biyo baya, yana da kyau mu lura da yadda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza cika alkawurran da ta yiwa 'yan Najeriya tun 2015.

"An samun karin rashin jituwa tsakanin kirista da sauran mabiya addinai, kashe-kashen mikiyaya ya karu kuma ana cigaba da yiwa mabiya addinin kirista kisan kiyashi.

Sace 'yan matan Dapchi da rashin karbo Leah Sharibu daga hannun 'yan ta'adda da kuma hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa a Metele, Baga da sauran garuruwa da kuma kashe-kashen jihar Kaduna, Yobe, Plateau da jihohin Zamfara inda ake sace sarakuna ana kashe su duk alamomi ne da ke nuna gwamnatin Buhari ta gaza."

Kungiyar ta ce a garuruwan da ake mutunta mutane, shugaban kasa da shugabanin hukumomin tsaro kamata ya yi suyi murabus saboda sun gaza wurin gudanar da aikin su na kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel