2019: Gwamnan APC ya ce jam'iyyar ba zata ci zabe a jihar sa ba

2019: Gwamnan APC ya ce jam'iyyar ba zata ci zabe a jihar sa ba

- Gwaman jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya ce jam'iyyar APC zata sha kaye a zaben gwamna a jiharsa

- Gwamnan ya ce dan takarar jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM), Adekunle Akinlade ne zai lashe zaben

- Gwamna Amosun ya so Mr Akinlade ne ya gaje shi amma Dapo Abiodun ya kayar da shi a zaben fidda gwani

Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya bugi kirji ya ce dan takarar gwamna na jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM), Adekunle Akinlade ne zai lashe zabe a jihar.

Mr Amosun ya kuma shawarci gwamnatin tarayya kada ta aike da sojoji zuwa jihar domin zabe duk da ya bayar da tabbacin za a gudanar da zaben lami lafiya.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a daren ranar Litinin a taron murnar shiga sabuwar shekara da akayi a Oke-Ilewo a garin Abeokuta.

2019: Gwamnan APC ya ce jam'iyyar ba zata ci zabe a jihar sa ba

2019: Gwamnan APC ya ce jam'iyyar ba zata ci zabe a jihar sa ba
Source: Depositphotos

Gwamna Amosun yana takarar kujerar sanata a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress amma yana goyon bayan Mr Akinlade wadda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APM bayan ya sha kaye a hannun Dapo Abiodun.

DUBA WANNAN: Atiku zai lallasa Buhari a yankin Arewa maso yamma - Kungiya

Mr Amosun ya ce na hannun damarsa, Mr Akinlade zai kayar da Mr Abiodun da sauran 'yan takarar gwamna a zaben da za a gudanar a watan Mayu.

Gwamnan mai barin gadon ya yi kira ga al'ummar jihar su rungumi zaman lafiya musamman a wannan lokacin da zabe ke qaratowa.

"Mu hada hannu wuri guda domin nunawa duniya cewa mu mutane ne masu son zaman lafiya kuma jiha ce wadda ta samar da fittatun mutane a Najeriya," a cewar Mr Amosun.

"Mu nuna musu cewa bamu bukatar sojoji ko 'yan sanda saboda zabe domin zamu gudanar da zaben mu cikin zaman lafiya da lumana. Sannan ku matasa, duk wanda ya nemi kuyi masa bangar siyasa ke fada masa ya turo yaransu kuyi bangar tare."

A yanzu da ya ke shirin barin mukaminsa na gwamna, Mr Amosun ya mika godiyarsa ga dukkan al'ummar jihar saboda irin gudunmawar da suka bashi har ta kai ga ya samu nasarorin da ya samu a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel