Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

- Shugaban cocin Brotherhood of the Cross and Star, Olumba Olumba Obu ya ce babban zaben shekarar 2019 zai girgiza Najeriya da duniya baki daya

- Olumba Obu ya ce amma girgizar ba na tashin hankali bane sai dai yadda Allah zai samar da zaman lafiya a dukkan sassan kasar

- Babban malamin ya shawarci 'yan Najeriya su yafe wa juna kuma su cigaba da kulawa da juna domin hakan ne zai kawo cigaba a kasar

Shugaban cocin Brotherhood of the Cross and Star, His Holliness Olumba Olumba Obu ya ce zaben shugabancin kasa da na gwamna da za ayi a shekarar 2019 zai girgiza duniya baki daya ba 'yan Najeriya kadai ba.

A sakon sa na shiga sabuwar shekara da ya fadi a hedkwatan cocinsa da ke Calabar, babban malamin addinin ya ce girgizar ba na tayar da hankali bane abinda ya ke nufi shine Allah zai samar da zaman lafiya a kasar.

Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini
Source: Twitter

Ya cigaba da cewa, wadanda suka yi nasarar lashe tikitin takarar a jam'iyyunsu ba sune za su kasance shugabanni ba bayan zaben sai dai wadanda Allah ya riga ya zabe su tuntuni.

DUBA WANNAN: Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da na hannun damar Ganduje daga mukaminsa

Ya yi kira ga al'ummar Najeriya su zauna lafiya, su yafe wa juna, su kula da juna sannan su cigaba da aikata ayyukan alkhairi domin ayyukan alkhairin ne zai janyo albarka a kasar baki daya.

Ya yi gargadi a kan kashe-kashen da ake yi a wasu sassan kasar nan da tashe-tashen hankula da akeyi a lokacin zabe.

"Babban zaben da za ayi a Najeriya a wata mai zuwa zai girgiza duniya da 'yan Najeriya tare da basu mamaki. Sai dai wadanda suke bauta wa Allah su kwantar da hankulan su. Allah ya riga ya dawo da zaman lafiya a Najeriya.

"Ya kamata 'yan Najeriya su koya zama lafiya da juna, su yafe wa juna kuma su rika kulawa da juna a shekarar 2019. Wannan shekarar, wasu da dama za su ga sakamakon ayyukan da suka yi," inji Obu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel