Karan kwana: Yadda wasu mutane 30 suka gamu da mummunan ajali a sabuwar shekara

Karan kwana: Yadda wasu mutane 30 suka gamu da mummunan ajali a sabuwar shekara

Akalla mutane Talatin ne suka gamu da ajalinsu a yayin da wata babbar motar daukan kaya watau Tirela ta tattakesu, daga cikinsu har da wata mata mai dauke da juna biyu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin, 31 ga watan Disamba, ranar karshe ta shekarar 2018 da misalign karfe 11:45 na dare, kimanin mintuna 15 gabanin shiga sabuwar shekarar 2019 a awon bature kenan.

KU KARANTA: Yajin aiki: Hakurin mu ya kusa karewa – ‘Dalibai sun fadawa Buhari da ASUU

Karan kwana: Yadda wasu mutane 30 suka gamu da mummunan ajali a sabuwar shekara

Jami'an hukumar FRSC
Source: Original

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewar mutanen su Talatin sun gamu da ajalinsu ne a daidai garin Gbagi tuntun dake kan babbar hanyar Ife zuwa Ibadan daga jahar Osun.

Sai dai majiyar ta bayyana cewar ana zargin direban babbar motar da kasancewa a halin maye da marisa a daidai lokacin da yake tukin motar, ma’ana sai da ya bankadi barasa kafin ya fara tukin, wanda wannan hali ne da aka san direbobin Najeriya da shi.

Amma dai zuwa lokacin tattara rahoton nan babu wani jawabi daga ofishin hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, reshen jahar Oyo ko kuma rundunar Yansandan jahar Oyo dangane da mummunan hadarin.

Irin wannan hadari ba sabon abu bane akan babbar hanyar Ibadan, inda ko a watan satumbar shekarar 2017 sai da aka kamanta wata kazamar hadari akan wannan hanya, wanda tayi sanadiyyar mutuwar mutane Talatin farat daya, tare da jikkata mutane goma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel