Gagarumin yajin aiki: Zamu gwabza da gwamnati akan karancin albashin N30, 000

Gagarumin yajin aiki: Zamu gwabza da gwamnati akan karancin albashin N30, 000

Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta yi ma ma’aikatan Najeriya albishirin shiga yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta gagara biyansu karancin albashin da aka amince za’a biya na naira dubu talatin, daga sabuwar shekarar 2019.

Legit.com ta ruwaito shugaban NLC, kwamared Ayuba Wabba ne ya sanar da haka a ranar Talata 1 ga watan Janairun shekarar 2019 a yayin da yake gabatar da sakon gaisuwar sabuwar shekarar 2019 ga ma’aikata a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Yajin aiki: Hakurin mu ya kusa karewa – ‘Dalibai sun fadawa Buhari da ASUU

Gagarumin yajin aiki: Zamu gwabza da gwamnati akan karancin albashin N30, 000

Ayuba Wabba
Source: Depositphotos

A cewar Ayuba, shekarar 2018 ta zamto shekara matsananciya ga ma’aikatan Najeriya, musamman duba da yadda gwamnatin Najeriya ta gagara biyan karancin albashin naira dubu talatin a shekarar, duk da amincewar kwamitin da shugaban kasa Buhari ya kafa don tattauna batun.

“Jan kafa da gwamnatin tarayya ke nunawa game da biyan sabon tsarin albashin ya lalata dangantaka tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin, don haka zamu iya fadawa gagarumin yajin aiki nan bada jimawa ba.

“Don haka muna kira ga gwamnatu da tayi duk abinda ya kamata daga bangarenta daya shafi gaggauta mika daftarin sabon tsarin albashin ga majalisun dokokin Najeriya domin su tattauna akanta, haka zalika muna kira ga ma’aikata da su zauna cikin shirin fadawa yajin aiki na dindindin.” Inji shi.

Ayuba Wabba ya cigaba da fadin shugabancin NLC a shirye yake su bada kare hakkokin ma’aikata tare basu nagartaccen jagoranci a yayin da suke gabanin shiga yajin aiki don kwatan hakkokinsu daga hannun gwamnati.

Daga karshe yayi barazanar NLC ba zata lamunci dokar hana ma’aikata albashinsu ba yayin da suka afka yajin aiki, da nufin illata ma’aikatan, sa’annan yace zasu jajirce har sai gwamnati ta biya kowanne ma’aikaci albashinsa da kuma kudaden yan fansho.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel