Dalilin da yasa na ke neman tazarce a karkashin inuwar PDP - Gwamna Ortom

Dalilin da yasa na ke neman tazarce a karkashin inuwar PDP - Gwamna Ortom

- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce PDP ta ce za ta bashi ikon aiwatar da ayyukan da ya ke son yiwa al'ummar jihar Benue

- Ortom ya ce ya zame masa dole ya fice daga APC domin ya koma jam'iyyar da za ta bashi damar aiwatar da tsare-tsarensa musamman kafa dokar hana kiwo a fili

- Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta taka rawar gani duk da rashin iasashen kudi da rikice-rikicen da suka rika faruwa tsakanin makiyaya da manoma a jihar

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce ya yanke shawarar sake neman takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP ne saboda jam'iyyar ce za ta bashi damar aiwatar da shirye-shiryen da ya ke son yiwa mutanen jihar Benue.

Ortom ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin a Makurdi yayin kaddamar da yakin neman zabensa na gwamna.

Dalilin da yasa na sauya sheka daga APC zuwa PDP - Gwamna Ortom

Dalilin da yasa na sauya sheka daga APC zuwa PDP - Gwamna Ortom
Source: Depositphotos

Gwamna Ortom ya lashe zaben gwamna ne karkashin jam'iyyar APC bayan ya rasa samun tikitin takara a PDP a shekarar 2014 amma kuma yanzu ya sake komawa jam'iyyar ta PDP.

"Ya zama dole mu bar wannan jam'iyyar mu nemi wanda za ta bamu damar aiwatar da shirye-shiryen da muke son yiwa al'umma musamman doka hana kiwo a fili da kafa wuraren kiwo na shekarar 2017," inji shi.

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

Ya bayyana rashin jin dadin sa kan yadda wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC su kayi ta kokarin dakile dokar hana kiwon da za ta kawo zaman lafiya mai dorewa tsakanin makiyaya da manoma a jihar Benue.

"Irin wadannan matsin lambar da wasu jiga-jigan gwamnati suka rika yi min ya tilasta ni barin jam'iyyar APC domin ba zan amince a zalunci mutane na ba.

"Wannan jam'iyyar ce muke neman zarce a karkashinta. Babu wanda zai sanya mu janye dokar hana kiwo saboda mun nemi amincewar mutanen Benue kafin mu kafa dokar," inji shi.

A martanin da ya mayar ga masu sukarsa, Ortom ya ce ya tabbuka abin azo a gani duba da irin halin rashin kudi da tashe-tashen hankula da jihar ta tsinci kanta a ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel