Buhari zai mulki Najeriya gaba da 2019 - Wani babban malamin addini

Buhari zai mulki Najeriya gaba da 2019 - Wani babban malamin addini

- Wani babban malamin addinin kirista, Manzo Christopher Owolabi ya yi tsokaci a kan tazarce shugaba Muhammadu Buhari

- A ranar Talata 1 ga watan Janairun 2019, Manzo Owolabi ya yi hasashen cewa Shugaba Buhari zai cigaba da mulkin Najeriya bayan shekarar 2019

- Ya shawarci 'yan Najeriya su cigaba da yiwa shugabaninsu addu'o'i domin Allah ne ke zaban shugabani ba wani mutum ba

Shugaban Cocin Christ Apostolic da ke Ori Oke Irapada, Prophet Christopher Owolabi ya yi hasashen cewa shugaba Muhammadu Buhari zai cigaba da mulkan Najeriya bayan shekarar 2019 a cikin hasashensa na sabuwar shekara.

Ya ce, "An bayyana min cewa gwamnatin da ke jagorancin kasar nan a yanzu za ta kasance a kan mulki har bayan 2019 kuma akwai abubuwan alkhairi da za su wanzu a fanin walwalar al'umma da tattalin arziki."

Buhari zai mulki Najeriya gaba da 2019 - Wani babban malamin addini

Buhari zai mulki Najeriya gaba da 2019 - Wani babban malamin addini
Source: Depositphotos

Owolabi ya yi wannan hasashen ne a wa'azi na musamman da cocinsa ta shirya na tarbar sabuwar shekara wadda aka yiwa lakabi da "Seeking for Nigeria’s Democratic Sustenance Beyond 2019", a garin Omu-Aran a jihar Kwara.

DUBA WANNAN: Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da na hannun damar Ganduje daga mukaminsa

Malamin addinin ya ce wannan hasashen ba ta da alaka da siyasa ko son abin duniya sai dai kawai ya bayyana abinda Allah ya bayyana masa ne a matsayin mafita ga kasar nan.

Ya kuma yi hasashen cewa za a samu cigaba a fannin tattalin arziki da walwala a rayuwar al'ummar kasar a cikin sabuwar shekarar inda ya ce shugabanin Najeriya suna bukatar addu'o'i daga yan kasa domin samun nasara kan yaki da rashawa.

Ya kuma ce zaben shugabanni a Najeriya ya wuce sannin mutane domin Allah ne ke zaban shugabani da ya ke so.

"Duk da yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta so yi, Allah ne kadai ke zabar wanda zai yi shugbanci kuma ya ke tafiyar da al'ammuran kasar," inji shi.

Owolabi kuma ya yi kira ga 'yan siyasa su bi dokokin da hukumar zabe ta shimfida a yayin da suka yakin neman zabensu har ma da lokacin kada kuri'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel