2019: Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a sake zaben sa - Ribadu

2019: Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a sake zaben sa - Ribadu

A yayin da babban zaben kasa na 2019 ke daf da gudana, Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC, bisa mahanga ta hasashe gami da fahimta, ya bayyana ra'ayin sa kan kudirin tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mallam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ya zayyana dalalai dangane da cancantar shugaban kasa Muhammadu Buhari, na samun tazarcen kujerarsa yayin babban zaben kasa da za a gudanar a watan gobe.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon shugaban hukumar EFCC ya shimfida dalilai da ya cancanci al'ummar Najeriya su fito kwansu da kwarkwata wajen kadawa shugaba Buhari kuri'un su domin ci gaba da jagorancin kasa tsawon wasu shekaru hudu masu gabatowa.

2019: Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a sake zaben sa - Ribadu

2019: Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a sake zaben sa - Ribadu
Source: Twitter

Ya ke cewa, shugaban kasa Buhari ya dukufa ba bu dare ba bu rana wajen kawo tsare-tsare masu tasirin inganta jin dadin rayuwar al'ummar kasar nan. Ya ce 'yan adawar shugaban Buhari za su sha kunyar gaske sakamakon rashin nasara da za su fuskanta yayin zaben.

Tsohon shugaban hukumar EFCC ya bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar da wata sabuwar kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari da kuma mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, da aka gudanar cikin babban birnin Yola na jihar Adamawa.

KARANTA KUMA: 'Yan kungiyar yakin neman zabe da Aisha Buhari ta kafa domin nasarar mijin ta a 2019

Ribadu wanda ya yi takarar kujerar shugaban kasa yayin zaben 2011 ya jaddada tsayuwar dakansa tare da dukkanin magoya bayan sa wajen marawa shugaba Buhari baya a zaben shugaban kasa da zai gudana cikin watan Fabrairu na gobe.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Ribadu ya nemi takarar kujerar gwamnan jihar sa ta Adamawa karkashin inuwa ta jam'iyyar APC yayin zaben fidda gwani da aka gudanar watanni kadan da suka gabata, sai da ya sha kashi a hannun gwamnan jihar mai ci a yanzu, Muhammad Jibrilla Bindow.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel