Atiku zai lallasa Buhari a yankin Arewa maso yamma - Kungiya

Atiku zai lallasa Buhari a yankin Arewa maso yamma - Kungiya

- Kungiyar hadin kan matasan yankin Arewa maso yamma na Atiku ta ce Atiku ne zai yi nasara a yankin a babban zaben 2019

- Shugaban kungiyar, Shuaibu ya ce masu kada kuri'u a yankin za su zabi Atiku saboda gwamnati mai ci yanzu ba ta kyauta musu ba

- Shuaibu ya ce kungiyar da za ta tabbatar cewa Atiku da sauran 'yan takarar jam'iyyar PDP suni nasara a yankin a zaben 2019

An bayyana cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne zai lashe kuri'un yankin Arewa maso yamma a babban zaben 2019 da ke tafe.

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar hadin kan matasan yankin Arewa maso yamma na Atiku ne su kayi hasashen cewa Atiku ne zai lashe kuri'un yankin a 2019.

Atiku zai lallasa Buhari a yankin Arewa maso yamma - Kungiya

Atiku zai lallasa Buhari a yankin Arewa maso yamma - Kungiya
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da na hannun damar Ganduje daga mukaminsa

Kungiyar tayi alkawarin samarwa Atiku da sauran 'yan takarar jam'iyyar PDP kuri'un da zai sanya suyi nasara a zaben da za a gabatar nan da makonni shida.

Kungiyar tayi wannan alkawarin ne a wurin bikin cika shekaru 7 da kafa ta a garin Kano.

Shugaban kungiyar, Abubakar Shuaibu ya yi ikirarin cewa abu mai sauki ne janyo hankulan mutane su zabi Atiku a yankin saboda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta jefa yankin cikin talauci da rashin tsaro.

Sai dai wannan ikirarin na kungiyar ya ci karo da gargadin da wani gwamnan PDP ya yiwa jam'iyyar inda ya ce akwai yiwuwar za su sha kaye a zaben shugabancin kasa a yankin.

Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnan ya ce muddin jam'iyyar ba ta magance wasu matsaloli da ke kawo cikas a yakin neman zaben ta ba za ta sha kaye.

Gwamnan da ya nemi a boye sunansa ya ce akwai matsaloli sosai tattare a shirye-shiryen yakin neman zaben shugabancin kasa na jam'iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel