Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN

Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN

- Shugaban kiristici yayi kira ga yan siyasa da hukumomin tsaro dasu yi aiki tukuru dan ganin anyi zabe lafiya

- Yayi wannan kira ne a sakon barka da sabuwar shekara daya tura

- Muna fata wannan shekara ta 2019 ta kasance shekarar zaman lafiya da kwanciyar hankali

Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN

Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN
Source: UGC

Shugaban kiristoci na Najeriya Rev(Dr)Samson Ayokunle yayi kira ga yan siyasa da hukumomin tsaro dasu yi aiki tukuru dan ganin an gudanar da zaben shekara ta 2019 lafiya.

Rev. Ayokunle yayi wannan kira ne a sakon barka da shigowa sabuwar shekara da ya tura.

Yayi kira ga yan Najeriya dasu kasance masu gaskiya a yayin gudanar da zaben ta hanyar zaben shugaban da yake ra'ayin su ne.

Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN

Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN
Source: Getty Images

Sakon mai taken "Nigeria's dry bones will rise again" yana dauke da sako kamar haka:

"A madadin kungiyar kiristoci ta Najeriya ( CAN) ina mika sakon barka da shigowa sabuwar shekara ga dukkanin yan Najeriya na gida da na ketare .

"Ina fatan wannan shekara ta 2019 ta kasance shekara ta zaman lafiya da kwanciyar hankali,sannan kasusuwan mu ta suka bushe zasu taso da yardar Allah ".

DUBA WANNAN: Aiki jaa a gaban Arewa, dubi yadda yawan talakawa da yake a jiha-jiha, kudu da arewa

"Shekara ta 2019 shekara ce ta kowanne dan Najeriya saboda a shekarar ne za'a gudanar da dukkanin wani zabe.ina kira ga yan Najeriya dasu gudanar da zaben cikin nutsuwa ba tare da sanya kansu cikin wata rigima ba kafin zaben da kuma bayansa".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel