Na tuka motar dana kera daga Legas zuwa Abuja domin in hadu da Buhari - Obasanjo

Na tuka motar dana kera daga Legas zuwa Abuja domin in hadu da Buhari - Obasanjo

- Obasanjo, ya ce ya tuka motar da ya kera daga Legas zuwa Abuja don haduwa da shugaban kasa Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo

- Motar, wacce a cewarsa, zata iya tafiya akan titi, ruwa da iska, ya kera ta ne kamar siffar jirgin sama mai dauke da fuka-fuki da farfeloli

- Obasanjo ya ce yana son haduwa da shugaban kasa da mataimakinsa don sanar dasu abunda ya faru da kuma yadda aka lalata motar

Wani d'an Nigeria wanda ya kware a bincike da kere kere, Durojaiye Kehinde Obasanjo, ya ce ya tuka motar da ya kera mai kama da jirgin sama, na tsawon awanni 15 daga Legas zuwa Abuja don haduwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Motar, wacce a cewarsa, zata iya tafiya akan titi, ruwa da iska, ya kera ta ne kamar siffar jirgin sama mai dauke da fuka-fuki da farfeloli, wanda ya tilasta wasu mazauna Abuja tururwa don kallon motar a okacin da ya shigar da ita birnin tarayyar.

Obasanjo, wanda ya ce zai fara zuwa hukumar bincike da tattalin sararin samaniya ta Nigeria don basu rahoton wanan ci gaba, ya fara yada zango a wasu tashoshin motoci da kuma kan hanyar filin jirgin sama, inda jama'a da dama suka nuna sha'awarsu ga motar tare da daukar hotuna a kusa da ita.

KARANTA WANNAN: PDP tayi Allah-wadai da gazawar Buhari na halartar jana'izar Shehu Shagari

Dalilin da yasa na tuka motar dana kera daga Legas zuwa Abuja - Obasanjo

Dalilin da yasa na tuka motar dana kera daga Legas zuwa Abuja - Obasanjo
Source: Twitter

Akan dalilin da ya sa yake da burin haduwa da shugaban kasa da mataimakinsa, Obasanjo ya ce: "Akwai motar da na kera da ya kamata ace an kerata da yawa a Nigeria don bunkasa tattalin arzikin kasar, sai dai wasu jami'an gwamnatin Legas sun lalatata cewar wai haramun ne na kera motar.

"Na kai karar hakan ga gwamna Ambode na Legas, kuma ya ce zasu nemeni, amma har yau basu kara tuntubata ba. Wannan ne yasa nazo Abuja don sanar da mahukuntan da ya dace akan wannan mota dana kera.

"Don haka, ina so na hadu da shugaban kasa da mataimakinsa don sanar dasu abunda ya faru da kuma yadda aka lalata motar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel