1-1-2019: A yau ne Najeriya zata farlanta aiki da tsarin NIN a kan kowacce hada-hada

1-1-2019: A yau ne Najeriya zata farlanta aiki da tsarin NIN a kan kowacce hada-hada

- Yau ce rana ta farko a 2019

- A yau tsarin NIN zai fara aiki

- Shugaba Buhari neya sahale wa shirin

1-1-2019: A yau ne Najeriya zata farlanta aiki da tsarin NIN

1-1-2019: A yau ne Najeriya zata farlanta aiki da tsarin NIN
Source: Instagram

Bayan shafe shekaru kusan 60 tun daga sanda turawa suka bamu mulkin mallaka, sai yanzu ne kasar Najeriya zata fara aiki da tsarin zamani na NIN, karkashin ofishin shugaban kasa, wanda ya tilastawa duk wani dan kasa aiki da lambar ta NIN kafin morar shiri ko ayyukan gwamnati.

NIN na nufin National Identiti Number, watau lambar da ake baiwa kowanne dan kasa in yayi katin zama dan kasa na NIMC, wadanda suka shafe shekaru 15 suna yiwa jama'a rajista.

Tsarin, zai baiwa gwamnati damar sanin suwaye 'yan kasa su waye bakin haure, zai kuma bada damar iya sanin mutane nawa ko moruwa da shirye-shirye da tsare-tsaren da gwamnatin keyi don talakawanta.

DUBA WANNAN: Ajandar Boko Haram: Ashe wai suna so su kwaci Damasak, Monguno da Abadam cikin makonnin nan ne

Karkashin tsarin, sai kana da ID card mai lambar gwamnati wanda NIMC ke bayar wa, sannan za'a ki hulda da gwamnati, a fannin lafiya ko makaranta ko samun filaye, in dai ka kai shekaru 18 kuma kai dan asalin Najeriya ne.

Hakan zai rage shige da ficen baki babu ka'ida, wasu ma su tare dungurungun a kasar nan, da ma masu fakewa da aikata laifi, ko hada-hadar kudi ta muggan hanyoyi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel