PDP tayi Allah-wadai da gazawar Buhari na halartar jana'izar Shehu Shagari

PDP tayi Allah-wadai da gazawar Buhari na halartar jana'izar Shehu Shagari

- Jam'iyyar PDP ta yi Allah-wadai da gazawar shugaban kasa Buhari na halartar jana'izar tsohon shugaban kasar Nigeriam Alhaji Shehu Shagari

- Jam'iyyar adawar ta ce gazawar Buhari na halartar jana'izar, ya nuna rashin dattako da bijirewa tsarin demokaradiyyar kasar

- Haka zalika, PDP ta ce wannan mataki na shugaban kasar abun haushi da takaici ne

Jam'iyyar PDP ta yi Allah-wadai da shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaza halartar jana'izar tsohon shugaban kasar Nigeria, Alhaji Shehu Shagari, a ranar Asabar, 29 ga watan Disambar 2018.

Jam'iyyar ta ce gazawar shugaban kasar na halartar jana'izar, musannan duba da irin martaba da matsayin Alhaji Shehu Shagari, a matsayi zababben shugaban Nigeria na farko, abun takaici da kunar rai ne, kuma wanda ya sabawa tsarin tarbiyar demokaradiyyar kasar.

A cewar PDP, wannan mataki na shugaban kasa Buhari ya aikawa kasashen waje wani mummunan sako na cewar Nigeria bata girmama magabata da shugabanci kasar, a bayan kushewarsu.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: ASUP ta bayyana dalilin da yasa ba zata janye yajin aiki yanzu ba

PDP tayi Allah-wadai da gazawar Buhari na halartar jana'izar Shehu Shagari

PDP tayi Allah-wadai da gazawar Buhari na halartar jana'izar Shehu Shagari
Source: UGC

Jam'iyyar a cikin wata sanarwa da ta aikewa jaridar Legit.ng a ranar Litinin, 31 ga watan Disamba, daga hannun sakataren watsa labaranta na kasa, Kola Ologbodiyan, PDP ta kuma yi Allah-wadai da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na gaza halartar jana'izar.

A cewar Ologbodiyan, gwamnatin shugaban kasa Buhari bata dauki wani kwakkwaran mataki na girmama Shagari ba, "in banda daukar jirgi da shugaban kasar yayi tare da tawaga zuwa Sokoto don yin ta'aziyyar kwanaki uku.

"Abun takaicin shine, a lokacin da tsohon shugaban kasarmu, Shagari, yake kwance akan gadon ajalinsa a babban asibitin Abuja, shi kuwa shugaban kasa Buhari, yana Uyo, jihar Akwa Ibom yana yakin zabe, inda yake ikirarin cewa shine ya tunbuke jamhuriyya ta biyu, tare da cafke Shehu Shagari da mukarraban gwamnatinsa, wanda hakan alama ce karara ta yin karan tsaye ga tarbiyar demokaradiyyar kasar."

A hannu daya kuwa PDP ta bukaci majalisar dokokin tarayya data karrama Shagari ta hanyar tursasa gwamnatin tarayya, akan canja sunan wata babbar makaranta a kasar zuwa sunan tsohon shugaban kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel