Dalilin da ya sanya ba za mu iya biyan N30,000 mafi karancin albashi ba - NGF

Dalilin da ya sanya ba za mu iya biyan N30,000 mafi karancin albashi ba - NGF

A yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana dangane da tabbatuwar sabon mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan, kungiyar gwamnonin Najeriya, Nigeria Governors' Forum NGF, ta yi karin haske tare da jaddada matsayar a kan hakan.

Dalilin da ya sanya ba za mu iya biyan N30,000 mafi karancin albashi ba - NGF

Dalilin da ya sanya ba za mu iya biyan N30,000 mafi karancin albashi ba - NGF
Source: Depositphotos

A jiya Litinin, gwamnonin Najeriya sun bayyana rashin kishin kisa na kungiyar kwadago dangane da ci gaba da fafutikar ta akan mafi karancin albashin ma'aikata na N30, 000 da ta jajirce ba bu gudu ba bu ja da baya.

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce hakan wani yunkuri ne na yiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari dabaibayi da kuma kasa baki daya kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

A yayin da gwamnonin suka bayyana soyayyar su ta biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata, sun kuma bayyana takaicin su dangane da rashin yiwuwar hakan sakamakon rashin wadatattun kudade na gudanar da ayyukan jihohin su da ya kawowa wannan lamari cikas

Shafin jaridar The Punch ya ruwaito cewa, kungiyar gwamnonin ta bayyana hakan ne da sanadin jami'inta na hulda da al'umma, Mista Abdurrazaque Bello Barkindo cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya gana da dan takarar kujerar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar APC a fadar Villa

Ta ke cewa, ba bu gaskiya dangane da ikirarin kungiyar kwadagon da sanadin babban sakataren ta, Mista Peter Eson, da ya bayyyana cewa gwamnonin sun hau kujerar naki kan biyan sabon mafi karancin albashin ma'aikata haka siddan ba tare da wasu dalilai ba.

Kazalika kungiyar gwamnonin ta jaddada matsayarta ta biyan N22, 500 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata da a cewar ta hakan shine gwargwadon iko da ba zai haura karfin ta ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel