Babbar magana: ASUP ta bayyana dalilin da yasa ba zata janye yajin aiki yanzu ba

Babbar magana: ASUP ta bayyana dalilin da yasa ba zata janye yajin aiki yanzu ba

- Kungiyar malaman kwalejojin koyar da sana'o'i (ASUP) ta ce bata da wani zabi da ya wuce ci gaba da yajin aikin da ta tsunduma tun a shekarar data gabata

- Wannan mataki da ASUP ta dauka, ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya na sakin N15bn don gyaran kwalejojin kamar yadda tayi alkawari a 2017

- ASUP ta ce tana fatan cewa za a haifi d'a mai ido a zaman da ta shirya gudanarwa da gwamnatin tarayya a ranar 10 ga watan Janairu don bitar yarjejeniyar

Kungiyar malaman kwalejojin koyar da sana'o'i (ASUP) ta ce bata da wani zabi da ya wuce ci gaba da yajin aikin da ta tsunduma tun a shekarar data gabata, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya na sakin N15bn don gyaran kwalejojin kamar yadda tayi alkawari a 2017.

Shugaban kungiyar ASUP na kasa, Usman Dutse, ya bayyana hakan a cikin wata zantawa da jaridar PUNCH a ranar Juma'a, cewar a yarjejeniyar da kungiyar tayi da gwamnati a 2009, an yi alkawarin sakin N603bn don gyaran kwalejojin, sai dai a yarjejeniyar 2017, saboda rashin kudi, gwamnati tayi alkawarin sakin N15bn daga cikin kudin.

Kungiyar malaman kwalejojin sun ce suna fatan cewa za a haifi d'a mai ido a zaman da shuwagabannin kungiyar suka shirya gudanarwa da gwamnatin tarayya a ranar 10 ga watan Janairu don bitar yarjejeniyar.

KARANTA WANNAN: 2019: Ganduje na da kashi 88 na yiyuwar lashe zabe - Kungiya

Babbar magana: ASUP ta bayyana dalilin da yasa ba zata janye yajin aiki yanzu ba

Babbar magana: ASUP ta bayyana dalilin da yasa ba zata janye yajin aiki yanzu ba
Source: Twitter

Kungiyar ASUP dai ta fara yajin aikinta na fadin kasar a ranar 12 ga watan Disamba, 2018, inda ta bayyana gazawar gwamnatin tarayya na cimma yarjejeniyar 2009, 2013 da 2017 a matsayin silar tafiyar kungiyar yajin aiki.

Dutse, ya shaidawa manema labarai cewa wasu gwamnatocin jihohi sun gaza biyan albashin malaman kwalejojinsu, inda ya kara da cewa har sai jihohin sun biya wadannan basussukan ne kungiyar zata duba yiyuwar janye yajin aikin.

Ya ce: "A rahoton binciken da NEEDS ta gudanar, gwamnati ta fara yin alkawarin sakin N603bn don gyaran kwalejoji. Amma saboda dogon lokacin da aka kwashe, farashin kayayyakin aiki suka canja, kuma akwai sabbin kwalejoji da aka gina, don haka aka sake bitar kudin, tare da cimma matsayar biyan N800bn. A lokacin babu wata hanya taka mai-mai da gwamnati ta ke da shi na samun wadannan kudade.

"Amma a shekarar 2017, a yarjejeniyar karshe, hgwamnati ta ce tana fuskantar karancin kudi da wasu matsaloli na tattain arziki, don haka zata iiya sakin N20bn ne kawai ga jami'o'i, yayin da zata sai N15 a kwalejojin koyar da sana'o'i, sai N15 ga kwalejojin ilimi.

"Tun 2017, ba a sakarwa kwalejoji wadannan kudade ba. Babban dalilin da ya sa muka kafe akan lallai sai an biya kudaden ba zai wuce tabbatar da gani cewa an cika wannan alkawari da aka yiwa kwalejoji a 2017 ba, sannan sai an biya N15bn dinne zau janye yajin aikin," a cewar Dutse.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel