Da dumi dumi: Aisha Buhari ta yi amai ta lashe, ta kafa kungiyar yakin zaben mijinta

Da dumi dumi: Aisha Buhari ta yi amai ta lashe, ta kafa kungiyar yakin zaben mijinta

- Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta yi amai ta lashe, kan barazanar da tayi a baya, na cewar ba zata goyi bayan mijinta Muhammadu Buhari ba

- Sai dai, a yanzu ta kafa kungiyar yakin tazarcen mijin nata, ba tare da tuna wannan barazana da tayi a baya ba

- A ranar Alhamis, ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wannan kungiya a Abuja, mai dauke da mutane 700

Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta yi amai ta lashe, kan barazanar da tayi a baya, na cewar ba zata goyi bayan mijinta Muhammadu Buhari ba, a kokarinsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na biyu, idan har bai gyara wasu abubuwa da ke faruwa a gwamnatinsa ba.

Uwar gidan Buhari ta jawo hankulan kasashen duniya a lokacin da ta caccaki mijinta a cikin watan Oktobar 2016, a wata hira da tayi da kafar watsa labarai ta BBC, inda ta ce tana tsoron cewar gwamnatin mijin nata ta kauce daga turbar da aka kafata na kawo sauki da canji ga 'yan Nigeria.

Haka zalika ta bayyana damuwarta da kuma kokontonta akan goyon bayan mijin nata don sake shugabantar kasar ko kuma bijire masa, inda ta ce zata goyi bayansa ne kawai idan har ya kawo sauye sauye a tsare tsaren gwamnatinsa.

KARANTA WANNAN: Idan har ana son kawo karshen Boko Haram, sai an sauke Buhari a 2019 - Atiku

Da dumi dumi: Aisha Buhari ta yi amai ta lashe, ta kafa kungiyar yakin zaben mijinta

Da dumi dumi: Aisha Buhari ta yi amai ta lashe, ta kafa kungiyar yakin zaben mijinta
Source: UGC

Sai dai, a yanzu za a iya cewa ta yi amai ta lashe, domin kuwa ta kafa kungiyar yakin tazarcen mijin nata, ba tare da tuna wannan barazana da tayi a baya ba.

Kungiyar da ta kafa, ta hada da uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, Sanatoci, matan gwamnoni, ministoci, tsofaffin gwamnoni, shuwagabannin hukumomi da kuma masu nishadantarwa, don tallafawa mijin nata a kokarinsa na tazarce a 2019.

Kungiyar yakin zaben wacce ke dauke da akalla mutane 700 da aka zabosu daga sassa daban daban na fadin kasar, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da ita a ranar Alhamis, a Abuja, a cewar kakakin Aisha, Suleiman Haruna.

Aisha ce zata jagoranci kungiyar da kanta yayin da matar mataimakin shugaban kasa zata zama shugaba ta biyu.

Mrs Adejoke O. Adefulure, da kuma uwar gidan gwamnan jihar Nasarawa, Mrs Mairo Al-Makura, sune zasu kasance mataimakan shugaban kungiyar na shiyyar Kudu da Arewa.

Haj. Salamatu Baiwa Umar – Eluma ita ce babbar kodinetar kungiyar ta kasa, Barr. Juliet Ibekaku-Nwagu (mataimakiyar kodineta ta kasa shiyyar Kudu) da kuma Hajiya Binta Muazu (mataimakiyar kodineta ta kasa Shiyyar Arewa).

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel