2019: Ganduje na da kashi 88 na yiyuwar lashe zabe - Kungiya

2019: Ganduje na da kashi 88 na yiyuwar lashe zabe - Kungiya

- Wata kungiya da ta shahara wajen hasashen zabuka mai suna 'Poll 4 Excellence, Africa (P4EA), ta ce Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai lashe zaben Kano da kashi 88

- Kungiyar ta taya Ganduje murnar wannan nasarar da ya samu a zaben data gudanar, wanda suka ce ya dauki tsawon watanni kafin aka kammala shi

- Kungiyar ta ce al'ummar jihar Kano sun bayyana gamsuwarsu kan irin salo shugabancin Ganduje da yadda yake tafiya da kowanne fannin ci gaba na jihar

Wata kungiya da ta shahara wajen hasashen zabuka mai suna 'Poll 4 Excellence, Africa (P4EA), mai shelkwata a Accra, Ghana, ta gudanar da zaben ra'ayoyin al'umma kan yiyuwar nasarar 'yan takarar gwamnan jihar Kano a 2019, inda daga karshe ta ce Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai lashe zaben da kashi 88.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da aka kaiwa gwamnan daga Accra, ta hannun wakilinsu da ke Abuja, dauke da sa hannun kodineta janar na kungiyar, Mr Ephraim Nonso, kana aka rabawa manema labarai a Kano, a ranar Litinin.

Kungiyar ta taya Ganduje murnar wannan nasarar da ya samu a zaben data gudanar, wanda suka ce ya dauki tsawon watanni kafin aka kammala shi. Haka zalika ta ce ta na kan gudanar da irin wannan zaben a jihohin Nigeria da dama, kuma nan ba da jimawa ba, sakamakon zaben jihohin zai bayyana ga jama'a.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Aisha Buhari ta yi amai ta lashe, ta kafa kungiyar yakin zaben mijinta

2019: Ganduje na da kashi 88 na yiyuwar lashe zabe - Kungiya

2019: Ganduje na da kashi 88 na yiyuwar lashe zabe - Kungiya
Source: Depositphotos

Kungiyar ta ce al'ummar jihar Kano sun bayyana gamsuwarsu kan irin salo shugabancin Ganduje da yadda yake tafiya da kowanne fannin ci gaba na jihar.

"Domin kawar da duk wani kokonto na samun nasarar wasu jam'iyyun adawa a jhar, musamman zargin da akewa gwamnan na cin hanci da rashawa, wasikar kungiyar ta bayyana cewa, nasarar da Ganduje ya samu a zaben da ta gudanar, ya bayyana irin soyayyar da al'ummar jihar Kano kemasa."

Kungiyar ta yi nuni da cewa ficewar Maam Ibrahim Shekarau daga jam'iyyar PDP, ya gurguntar da jam'iyyar, tare da baiwa APC damar samun kwarin guiwar nasara a zabe mai zuwa. Haka zalika da yawa na ganin cewa dan takarar PRP na jihar, Salihu Sagir Takai, ba zai kai labari ba ganin cewa ya guji uban gidansa Shekarau.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel