Kasafin 2019: Buhari zai kashe N1.98n kan abinci da tafiye tafiye

Kasafin 2019: Buhari zai kashe N1.98n kan abinci da tafiye tafiye

- Gwamnatin tarayya ta gabatar da N1,001,318,171 a matsayin kudin da Buhari yake bukata don yin tafiye tafiyen cikin gida dana kasashen waje

- A karkashin abinci da abun sha kuwa, an ware N98,306,492 a matsayin kudin abinci da kayan makulashe na shugaban kasar

- Haka zalika, an ware N83,974,71 a cikin kasafin kudin, a matsayin kudin da mataimakin shugaban kasa zai yi amfani da shi wajen tafiye tafiyen cikin gida

Gwamnatin tarayya ta gabatar da N1,001,318,171 a matsayin kudin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake bukata don yin tafiye tafiyen cikin gida dana kasashen waje a cikin kasafin 2019 da shugaban kasar ya gabatarwa majalisar dokokin tarayya.

Kasafin ya warewa shugaba kasar N250,021,595 a matsayin kudin tafiye tafiyen cikin gida, yayin da N751,296,576 a matsayin kudin tafiye tafiye zuwa kasashen waje, a cikin shekarar 2019.

Haka zalika, an ware N83,974,71 a cikin kasafin kudin, a matsayin kudin da mataimakin shugaban kasa zai yi amfani da shi wajen tafiye tafiyen cikin gida, yayin da aka ware masa N217,060,883 a matsayin kudin tafiye tafiye zuwa kasashen waje.

KARANTA WANNAN: Ba gaskiya bane cewar Dangote na cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa

Kasafin 2019: Buhari zai kashe N1.98n kan abinci da tafiye tafiye

Kasafin 2019: Buhari zai kashe N1.98n kan abinci da tafiye tafiye
Source: Facebook

A karkashin abinci da abubuwan sha kuwa, an ware N98,306,492 a matsayin kudin abinci da kayan makulashe na shugaban kasar, yayin da aka warewa mataimakin shugaban kasar N50,888,218 a matsayin kudin abincinsa da makulashe.

Haka zalika, gwamnatin tarayya ta gabatar da N416,668,229 a matsayin kudin da za a kashe don gina cibiyar kiwon lafiya a sashen shugaban kasar da ke cikin Aso Koro, daga cikin N49,307,859,794 da aka warewa fadar shugaban kasar a kasafin 2019.

Banda wannan, an ware N823,441,66 a matsayin kudin kula da cibiyar kiwon lafiya dake cikin fadar shugaban kasa, da suka hada da samar da magunguna da sauran kayan kiwon lafiya na akalla N208,350,424.

Idan za a iya tunawa a kasafin 2018, fadar shugaban kasa ta ware N1,030,458,453 don kula da cibiyar kiwon lafiya dake cikin fadar shugaban kasar, bayan da uwar gidan shugaban kasar, Mrs Aisha Buhari, ta kalubalanci asibitin na cewar babu ko allura a ciki.

A shekarar 2017 kuwa, an ware N3.2bn don ganin an daga darajar cibiyar kiwon lafiyar, inda ya hada da kammala sashen samar da magunguna da ajiyar sauran kayayyakin kiwon lafiya da ke cikin cibiyar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel