Girman banza: An kama wani mutum mai shekaru 52 da ya yiwa yaro mai shekaru 11 fyade Kaduna

Girman banza: An kama wani mutum mai shekaru 52 da ya yiwa yaro mai shekaru 11 fyade Kaduna

Wani ma'aikacin gwamnati mai shekaru 52, Mohammed Lawal Ahmed ya shiga hannun hukuma saboda samunsa da yiwa wani yaro mai shekaru 11 a duniya fyade a jihar Kaduna.

Daily Trust ta gano cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Disamba misalin karfe 9 na safiya a gidansa da ke CU2, Ikara Road, Sabon Gari, Tudun Wada a karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

Cikaken bayanin abinda ya aikata yana dauke cikin wani sako da hukumar tsaro da NSCDC ta aka aike wa Kotun Majistare da ke Kawo a Kaduna.

Girman banza: An kama wani mutum mai shekaru 52 da ya yiwa yaro mai shekaru 11 fyade Kaduna

Girman banza: An kama wani mutum mai shekaru 52 da ya yiwa yaro mai shekaru 11 fyade Kaduna
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

NSCDC ta ce wanda ake zargin ya yi amfani da kudi da alawa wurin janyo hankalin yaron zuwa gidansa inda ya rika sanya yatsunsa cikin duburan yaron har sai daga bisani da mahaifiyar yaron ta shigar da kara bayan lura da wasu abubuwa game da dan ta.

A yayin da majiyar Legit.ng ta nemi karin bayani daga wurin Kwamishinan Mata da Cigaban al'umma na jihar, Hajiya Hafsat Baba, ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce doka zaiyi aiki kan wanda ake zargi.

Ta ce abin takaici ne magidanci wadda ke da mata da yara zai aikata wannan mummunan aiki ga yaran wasu.

"Shari'ar na gaban kotun Majistare. Kotu ce za ta yanke hukunci amma duk da haka ma'aikatar matan za ta rika bibiyar shari'ar har an kammala.

"Dole ne a dena aikata duk wasu abubuwa na cin zarfin yaran mu a Kaduna musamman yanzu da muke da dokoki da za su hukunta masu laifi," inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel