Hisbah ta kama wani saurayi da ya yiwa 'yan mata 3 a gida daya fyade

Hisbah ta kama wani saurayi da ya yiwa 'yan mata 3 a gida daya fyade

- Matsalar yiwa mata, manya da kanana, fyade na kara ta'azzara a fadin Najeriya

- Kungiyoyi da dama na cigaba da kira ga mahukunta a kan kirkirar hukunci mai tsauri a kan masu fyade

- Jami'an Hisbah jihar Kano sun sanar da kama wani matsahi mai shekaru 23 da laifin yiwa 'yan mata uku fyade

Jam'ian Hisbah a jihar Kano sun sanar da cewar sun kama Suleiman Musa, matashi mai shekaru 23, bisa zarginsa da yiwa 'yan mata uku a gida daya fyade.

Majiyar Legit.ng ta shaida mata cewar lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba, a unguwar Kurnar Asabe dake garin Kano.

Musa ya zo unguwar ta Kurna ne a matsayin almajiri kafin daga bisani iyayen yaran su dauke shi yake masu aikin gida.

Hisbah ta kama wani saurayi da ya yiwa 'yan mata 3 a gida daya fyade

Jami'an Hisbah
Source: Twitter

Wani makobcin gidan da abin ya faru ya shaida wa majiyar mu cewar Musa ya yi amfani da yardar da iyayen yaran suka nuna masa wajen aikata laifin.

Kazalika ya bayyana cewar an kama Musa ne yayin da yake cikin lalata da daya daga cikin yaran.

A cewar makobcin, bayan an kama Musa ne aka gano cewar ya dade yana aikata haka ga yaran ta hanyar yi masu barazanar cewar zai yanka su idan suka fada wa iyayen su.

DUBA WANNAN: Boko Haram: Rundunar soji ta gargadi wasu mutane da kakkausar murya

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma'a, Abubakar Salihu, kwamandan Hisbah a karamar hukumar Dala, ya ce Musa na yin amfani da wuka domin tsorata yaran da yake yiwa fyaden.

Ya kara da cewa sun kai daya daga cikin yaran asibiti kuma an tabbatar da cewar an yi mata.

Da yake magana da manema labarai, Musa ya amsa laifinsa.

"Eh, na aikata hakan. Babu musu. Ban yiwa kaina adalci ba kuma ban kyauta ba. Ina addu'ar neman Allah ya shirye ni tare da masu irin wannan hali," a cewar Musa.

Wani jami'in hukumar Hisbah ya ce tuni sun mika mai laifin ga jami'an rundunar 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel