Yanzu-Yanzu: Wani dan majalisar tarayyar Najeriya ya rasu a asibitin Legas

Yanzu-Yanzu: Wani dan majalisar tarayyar Najeriya ya rasu a asibitin Legas

Labarin da muke samu da dumin sa yanzu shine na wani dan majalisar wakilan Najeriya dake wakiltar mazabar Ibeju-Lekki mai suna Hon Kabiru Abayomi Ayeola da ya rasu bayan 'yar gajeruwar rashin lafiya a wata asibiti dake a garin Legas.

Kamar dai yadda muka samu, dan majalisar ya rasu ne da yammacin ranar Lahadi 30 ga watan Disemba.

Shi dai Hon Kabiru Abayomi Ayeola kafin rasuwar sa yana wakiltar mazabar sa ne kuma dan jam'iyyar APC ne kuma ya rasu ne yana da shekaru 60 a duniya.

Kawo yanzu dai bamu samu cikakken bayani ba akan ainahin hakikanin rashin lafiyar da yayi fama da ita ba.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel