2019: Atiku na kulle-kullen shigowa da makudan kudi - BMO

2019: Atiku na kulle-kullen shigowa da makudan kudi - BMO

Kwamitin yada labaran kamfen din Buhari (BMO) ya yi ikirarin cewar ya bankado wani shiri da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ke yi na shigowa da wasu makudan kudi domin amfani da su yayin zaben shekarar 2019.

Kazalika kungiyar ta bukaci babban bankin kasa CBN) da hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) da su saka ido sosai musamman a kan iyakoki domin ta nan ne za a shigo da makudan dalolin.

A sanarwar da shugaba Niki Akinsiju da sakatare Cassidy Madueke suka sanya wa hannu, BMO ta ce ana son shigowa da kudin ne domin ganin an yi amfani da su wajen kayar da gwamnatin APC.

"Muna da sahihan bayanai dake nuna cewar jam'iyyar PDP da dan takarar ta na shugaban kasa na kokarin shigo da wasu haramtattun kudi da aka boye a kasashen waje domin a yi amfani da su wajen zaben shugaban kasa a 2019," a cewar sanarwar.

2019: Atiku na kulle-kullen shigowa da makudan kudi - BMO

Atiku d Buhari
Source: Twitter

Kungiyar ta cigaba da cewa, "saboda matakan tsaro da sabbin tsari da shugaba Buhari ya kawo a bangaren tattalin arziki, jam'iyyar PDP da dan takarar su na neman haramtattun hanyoda zasu yi amfani da su domin shigo da kudaden."

Sai dai a wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar Murtala Nyako, tsohon gwamnan jihar Adamawa, ya ce jam'iyyar APC mai mulki zata fadi zabe a jihohi da dama saboda rashin adalci da ya saka mambobinta da dama yin fushi da ita.

DUBA WANNAN: Ministan Buhari ya halarci bikin gargajiya daga shi sai dan kamfai, hotuna

Da yake magana da manema labarai bayan sauka a filin jirgi a Yola bayan ya dawo daga duba lafiyar sa a kasar waje, Nyako ya ce jam'iyyar APC ita ce ta talaka amma yin burus da bukatun jama'a da kuma rashin yin sulhu tsakanin mambobinta da suka fusata, ya rage mata farinjini.

Ya ce tunda jam'iyyar APC ta bar turbar adalci ta hanyar yin watsi da damuwar mambobinta, dole ta fuskanci matsala.

Ya kara da cewa matsalolin jam'iyyar APC sun samo tushe ne daga zabukan shugabanni da ta yi a fadin kasar nan. Nyako ya ce rashin adalcin da mahukuntar APC suka nuna a zabukan sabbin shugabannin ne ya fara kawo kawo baraka a cikinta.

Tsohon gwamnan ya ce da jam'iyyar APC ta saurari shawarar dattijai yayin gudanar da zabukan, da ba zata shiga matsalolin da ta ke ciki ba yanzu.

Tsohon jigo a jam'iyyar, ya cigaba da cewar APC kullum daddare wa take yi kuma ga zabe na kara matsowa, lamarin da ya ce ko shakka babu zai shafi nasarar jam'iyyar a zabukan shekarar 2019.

Nyako, daya daga cikin manyan 'yan siyasa masu farin jini da yawan mabiya a jihar Adamawa da yakin arewa maso gabas, ya ce rashin daukan shawarar da suka bawa jam'iyyar APC ne ya saka ta cikin halin da take ciki yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel