APC zata sha kaye a jihohi da yawa - Murtala Nyako

APC zata sha kaye a jihohi da yawa - Murtala Nyako

Murtala Nyako, tsohon gwamnan jihar Adamawa, ya ce jam'iyyar APC mai mulki zata fadi zabe a jihohi da dama saboda rashin adalci da ya saka mambobinta da dama yin fushi da ita.

Da yake magana da manema labarai bayan sauka a filin jirgi a Yola bayan ya dawo daga duba lafiyar sa a kasar waje, Nyako ya ce jam'iyyar APC ita ce ta talaka amma yin burus da bukatun jama'a da kuma rashin yin sulhu tsakanin mambobinta da suka fusata, ya rage mata farinjini.

Ya ce tunda jam'iyyar APC ta bar turbar adalci ta hanyar yin watsi da damuwar mambobinta, dole ta fuskanci matsala.

Ya kara da cewa matsalolin jam'iyyar APC sun samo tushe ne daga zabukan shugabanni da ta yi a fadin kasar nan. Nyako ya ce rashin adalcin da mahukuntan APC suka nuna a zabukan sabbin shugabannin ne ya fara kawo baraka a cikinta.

APC zata sha kaye a jihohi da yawa - Murtala Nyako

Murtala Nyako
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya ce da jam'iyyar APC ta saurari shawarar dattijai yayin gudanar da zabukan, da ba zata shiga matsalolin da ta ke ciki ba yanzu.

DUBA WANNAN: An lalata fastoci da allunanan tallar Atiku a jihar APC dake arewa

Tsohon jigo a jam'iyyar, ya cigaba da cewar APC kullum kara ragargaje wa take yi kuma ga zabe na kara matsowa, lamarin da ya ce ko shakka babu zai shafi nasarar jam'iyyar a zabukan shekarar 2019.

Nyako, daya daga cikin manyan 'yan siyasa masu farin jini da yawan mabiya a jihar Adamawa da yakin arewa maso gabas, ya ce rashin daukan shawarar da suka bawa jam'iyyar APC ne ya saka ta cikin halin da take ciki yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel