Naji godewa Allah da muka sasanta tsakanin mu ni da Shagari kafin rasuwar sa - Buhari

Naji godewa Allah da muka sasanta tsakanin mu ni da Shagari kafin rasuwar sa - Buhari

Shugaban kasar Najeriya kuma jagoran jam'iyyar mai mulki ta APC watau Muhammadu Buhari ya bayyana godiya ga Allah cewa dangantakar da ke tsakaninsa da marigayi Alhaji Shehu Aliyu Shagari tsohon shugaban kasar mai cikakken iko na farko ta gyaru.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar don bayyana alhininsa game da rasuwar Shehu Shagari. Ya ce duk da bambancin ra'ayi a kan wasu batutuwa, amma sun yi nasarar gyara alakar da ke tsakaninsu.

Naji godewa Allah da muka sasanta tsakanin mu ni da Shagari kafin rasuwar sa - Buhari

Naji godewa Allah da muka sasanta tsakanin mu ni da Shagari kafin rasuwar sa - Buhari
Source: UGC

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun murkushe harin 'yan Boko Haram a Baga

Legit.ng Hausa ta samu cewa Shugaban ya kuma bayyana Marigayin da kamilin mutum dan kishin kasa da ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannoni da dama wajen ciyar da kasa gaba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Muhammadu Buhari ne dai ya jagoranci kifar da gwamnatin marigayi Shehu Shagari lokacin yana babban hafsan soja a 1983. Sai dai a cikin sanarwar, Buhari ya ce mutuwar Shehu Shagari, wani babban rashi ne ga Najeriya.

A cewarsa, Najeriya ta yi asarar wata gada wadda ke hada dangantaka tsakanin tsoffin 'yan kishin kasa da suka yi fafutukar kwato 'yancin kai da kuma 'yan baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel