An lalata fastoci da allunanan tallar Atiku a jihar APC dake arewa

An lalata fastoci da allunanan tallar Atiku a jihar APC dake arewa

An lalata allunanan talla da ragowar fastocin kamfen din dake Lokoja da ragowar sanatoriyar jihar Kogi.

Shugaban sashen yada labarai na kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP (PDP-PCC0), Austin Usman, ya ce suna zargin magoya bayan jam'iyyar APC da aikata wannan barna.

Kazalika ya zargi gwamnatin jihar Kogi da daukan nauyin wadanda suka yiwa PDP hakan domin dakile adawar da suke fuskanta daga jam'iyyar.

An lalata fastoci da allunanan tallar Atiku a jihar APC dake arewa

An lalata fastoci da allunanan tallar Atiku a jihar APC dake arewa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

"Bayanan da muke da su sun nuna kuru-kuru cewar gwamnatin jihar Kogi ta dauki nauyin wasu batagari don kawai su lalata allunan tallar jam'iyyar PDP dake fadin jihar," a cewar sa.

"Da mun dauka rahoton ba gaskiya bane amma bayan ganin yadda aka fara lalata allunan tallar PDP daga Otokiti dake kan titin zuwa barikin soji da sauran allunan mu dake Koton Karfe da kan hanyar zuwa Lokoja, bamu da zabi da ya wuce tilas mu yarda da hannu gwamnati a cikin abinda ke faruwa."

Jam'iyyar PDP ta roki rundunar 'yan sanda, malaman addinai da masu rike da sarautar gargajiya da su shiga tsakaninsu da gwamnatin jihar a kan abinda ke faruwa.

Kokarin majiyar mu na jin ta bakin Kingsley Fanwo, kakakin gwamnan jihar Kogi a kan wannan batu, bai samu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel