Boko Haram: Rundunar soji ta gargadi wasu mutane da kakkausar murya

Boko Haram: Rundunar soji ta gargadi wasu mutane da kakkausar murya

- Aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram na kara tsananta a 'yan kwanakinnan a jihohin Borno da Yobe

- Dakarun sojin Najeriya sun dakile yunkurin 'yan ta'addar kungiyar na kwace karamar hukumar Bama

- Rundunar soji ta koka a kan halin wasu mutane da tayi zargin na yunkurin kawo rudani da tashin hankali

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewar ta fahimci wasu mutane marasa kishi dake ciki da wajen jihar Borno na kokarin jawo tashin hankali da kawo cikas ga aiyukan agaji saboda wasu dalilai da sune suka san su.

Rundunar ta ce ta samu rahoton cewar mutanen na zuga mazauna garuruwan Bama, Dikwa, da Monguno da su kauracewa gidajensu su koma sansanin 'yan gudun hijira ba tare da wani dalili ba.

Boko Haram: Rundunar soji ta gargadi wasu mutane da kakkausar murya

Boko Haram: Rundunar soji ta gargadi wasu mutane da kakkausar murya
Source: Facebook

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

Sai dai rundunar soji mai aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno ta Ofireshon Lafiya Dole ta bukaci jama'ar wadannan garuruwa da su yi watsi da wannan zuga, su kuma kwantar da hankalinsu.

A sanarwar da Onyema Nwachukwu, mataimakin darektan hulda da jama'a na rundunar Ofireshon Lafiya Dole ya fitar, ya ce zasu yi karin bayani a kan wannan lamari a ganawar da zasu yi da gwamnatin jihar Borno a gobe, Litinin, 31 ga watan Disamba.

Kazalika sun shawarci jama'a da su kwantar da hankalinsu tare da basu tabbacin kare su daga hare-haren ta'addanci na kungiyar Boko.

"Muna gargadin masu yunkurin kawo rudani da tashin hankali da su sani cewar idonmu na kansu", kamar yadda sanarwar ta kunsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel