Wata gobara mai daure kai ta kone gawarwaki a dakin ajiya

Wata gobara mai daure kai ta kone gawarwaki a dakin ajiya

Gawarwaki da yawa sun kone sakamakon gobarar da ta afku a wani sashi a dakin ajiye gawarwaki na asibitin Enugwu-Ukwu da ke karamar hukumar Njikoka da ke jihar Anambra.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa gobarar da afku ne misalin karfe 5.40 na yammacin ranar Asabar 29 ga watan Disambar 2018.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar Anambra, Haruna Muhammad ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce, 'yan sanda sun fara bincike domin gano abinda ya haifar da gobarar.

Wata gobara mai daure kai ta kone gawarwaki a dakin ajiya

Wata gobara mai daure kai ta kone gawarwaki a dakin ajiya
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kiwon Lafiya: Nau'o'in abinci 5 da za su kare ka daga kamuwa da mura

"Tawagar 'yan sanda karkashin jagorancin DPO na yankin Nimo, CSP Benjamin Egu ya kira jami'an kwana-kwana bayan ya isa wurin kuma daga bisani aka kashe wutar tare da taimakon mazauna unguwar.

"Sai dai, gobarar ya yi asara sosai kafin a kashe wutan ta kai ga kussan dukkanin gawarwakin sun kone ta yadda ba a iya gane su.

"Har yanzu dai ba a gano abinda ya janyo gobarar ba amma an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin afkuwar gobarar," inji CSP Muhammed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel