Idan aka sake zaben mu ba za ayi da-na-sani ba – inji Buhari

Idan aka sake zaben mu ba za ayi da-na-sani ba – inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Mutanen Najeriya ba za su yi nadamar kada masa kuri’a a 2019 ba, idan har su ka zabe sa ya zarce kan karagar mulki a karkashin jam’iyyar APC.

Idan aka sake zaben mu ba za ayi da-na-sani ba – inji Buhari

Shugaba Buhari ya nemi mutane su sake zaben sa a 2019
Source: Facebook

Shugaban kasar ya fadawa jama’a cewa ko kadan ba za su yi da-na-sanin sake zaben sa a karo na biyu ba. Buhari ya bayyana wannan ne a wajen wani babban kamfe da jam’iyyar APC ta shirya a Garin Uyo a cikin jihar Akwa Ibom.

Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa tayi maganin Boko Haram wanda a baya ta mamaye kananan hukumomi da dama a Najeriya. Buhari yace idan ya kuma zarcewa a kan mulki, zai karasa lallasa ‘Yan ta’addan.

Shugaban kasar ya tunawa mutane cewa ya cika manyan alkawuran da ya dauka na babbako da tattalin arzikin kasa da kuma inganta tsaro da yaki da sata. Yace an ga cigaba ta fuskar tattalin arziki bayan da aka koma amfani da TSA a Najeriya.

KU KARANTA: An yi kira ga Matasa su zabi jam’iyyar PDP daga sama har kasa a 2019

Shugaban ya tabbatar da cewa asusun bai-daya na TSA da aka kafa yana taimakawa wajen gano kudin da aka sace daga asusun Najeriya. Wadannan cigaba da aka samu ya sa shugaban kasar ya nemi mutane su sake zaben sa a 2019.

Sauran wadanda su ka halarci wannan gangami da aka yi a filin wasa na Garin Uyo sun hada da shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole, da kuma jigon jam’iyyar watau Bola Tinubu da kuma manyan Ministoci irin su Rotimi Amaechi.

‘Yan takaran APC a Jihohin Yankin; Nsima Ekere, Sanata John Eno, Delta, Great Ogboru, da kuma Tonye Cole sun karbi tuta a hannun shugaba Buhari. Haka kuma tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio yayi magana a wajen taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel