Zaben 2019: Da kyar Buhari zai zarce a kan karagar mulki – Mike Ahamba

Zaben 2019: Da kyar Buhari zai zarce a kan karagar mulki – Mike Ahamba

Wani babban Lauya da ake ji da shi kuma Dattijo a Najeriya, Cif Mike Ahamba yayi wata hira da jaridar kasar nan ta Sun kwanan nan, inda ya tattauna game da abubuwan da su ka shafi zaben da za ayi a 2019.

Zaben 2019: Da kyar Buhari zai zarce a kan karagar mulki – Mike Ahamba

Mike Ahamba SAN yace Atiku zai tika Buhari da kasa a 2019
Source: Facebook

Cif Mike Ahamba SAN ya bayyana cewa ba dole bane jam'iyyar APC ta sake komawa kan mulki a zaben 2019. Ahamba yake cewa jam’iyyar za ta gamu da kalubale sosai a irin su jihohin Imo inda rikici yake neman keta jam’iyyar.

Babban Lauyan kasar yake cewa ba ya tunanin cewa Atiku zai sha wahala wajen doke shugaba Buhari, domin kuwa wannan karo, Atiku zai yi takara ne ‘Dan Arewa. Ahamba yace kuri’un APC a Arewa zai ragu a zaben na 2019.

KU KARANTA: Hukumar INEC ta kara nuna dar-dar game da shirin zaben 2019

Lauyan ya kuma ce PDP za ta samu kuri’u mai tsoka a Kudancin Najeriya don haka yake ganin zai yi wa Buhari wahala ya iya zarcewa a kan mulki. Bayan nan kuma Lauyan yace Atiku ya shriya kuma ya cancanta da mulkin kasar.

Mike Ahamba SAN, ya na mai tabbacin cewa Atiku Abubakar ne mutumin da zai iya babbako da tattalin arzikin Najeriya ganin irin yadda arzikin kasar ya sukurkuce. A cewar sa, ‘Dan takarar na PDP ne zai yi nasara a zaben da za ayi a badi.

A hirar da Lauyan yayi, ya bayyana cewa zai fi sauki mutanen Ibo su samu mulkin Najeriya a tafiyar PDP a kan jam’iyyar APC. Ahamba ya kuma nuna shakku game da yadda INEC za ta gudanar da zaben na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel