Da dumin sa: Sojojin Najeriya sun murkushe hare-haren Boko Haram a Baga

Da dumin sa: Sojojin Najeriya sun murkushe hare-haren Boko Haram a Baga

Mahunta a rundunar sojin saman Najeriya sun ce sun murkushe wasu munanan hare-haren mayakan 'yan ta'addan Boko Haram a garin Baga dake zaman daya daga cikin garuruwan jihar Borno da ya sha fama da tashe-tashen hankula.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Ibekunle Daramola ya fitar, inda ya bayyana cewa bayan harin da mayakan Boko Haram suka kaddamar kan sojojin kasar, rundunar ta aika da jiragen yaki da suka fatattaki mayakan.

Da dumin sa: Sojojin Najeriya sun murkushe hare-haren Boko Haram a Baga

Da dumin sa: Sojojin Najeriya sun murkushe hare-haren Boko Haram a Baga
Source: Twitter

KU KARANTA: Na cika alkawurran da na daukarwa 'yan Najeriya a 2015

Legit.ng Hausa ta samu cewa a washegarin kirsimeti ne watau 26 ga watan Disemba mayakan Boko Haram suka shiga garin Baga suka yi musayar wuta da na sojojin Najeriya inda wasu rahotanni suka ce har kwace ikon garin tare da kafa tuta.

Sai dai a sanarwar da rundunar sojin ta fitar mai dauke da hoton bidiyo ta ce jiragen yaki da suka hada da masu saukar angulu sun kai wa sojojin dauki inda kuma suka fafattake su daga garin na Baga. Wasu bayanai na cewa mayakan sun kafa tuta a garin na Baga bayan sun shafe daren Laraba suna fafatwa da sojoji da ke garin.

Wani mazaunin gairn da ya shaida lamarin yace 'yan Boko Haram din sune ke iko da garin, domin sun kafa tuta, sannan babu wani soja ko da ya da ya rage a cikin garin.

Ya bayyana wa majiyar mu cewa mayakan sun afkawa wani babban sansanin soji da ke gefen ruwa a garin na Baga. Rundunar Sojin Najeriya dai ta ce mayakan Boko Haram din na buya a garin Baga da kewaye kuma dakarunta na kokarin gano su.

Rundunar ta kuma ce an tura karin sojojin ruwa da na kasa don samun karin karfin korar 'yan ta'addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel