Zan mika kaina ga 'yan sanda mako mai zuwa - Dino Melaye

Zan mika kaina ga 'yan sanda mako mai zuwa - Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye ya sake yin tsokaci kan mamaye gidansa da 'yan sanda su kayi

- Melaye ya ce baya Abuja a halin yanzu amma zai kai kansa ofishin 'yan sanda a cikin mako mai zuwa

- 'Yan sandan sun mamaye gidan Melaye da ke Abuja kuma sun ce ba za su tafi ba har Sanatan ya mika kansa

Sanata Dino Melaye mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawa ya yi alkawarin mika kansa ga 'yan sanda cikin mako mai zuwa.

A cewar Channels TV, A ranar Juma'a 28 ga watan Disamba, dan majalisar ya ce babu laifin da ya aikata saboda haka babu wani dalilin da zai sa ya rika kauracewa 'yan sanda.

Ya ce babu bukatar 'yan sandan su mamaye gidansa domin zai mika kansa ga jami'an 'yan sanda da zarar ya dawo garin Abuja.

Zan mika kaina ga 'yan sanda mako mai zuwa - Dino Melaye

Zan mika kaina ga 'yan sanda mako mai zuwa - Dino Melaye
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: APC ta mika sakon ta'aziyya ga PDP bisa rasuwar mambobinta da su kayi hatsarin mota

"An sanar da ni cewa 'yan sanda sun mamaye gida na. Fiye da 'yan sanda 40 suna cikin harabar gida na yayin da wasu 50 suna waje. An ci zarafin ma'aikata na wasu an doke su kuma an tafi da su.

"A halin yanzu bana garin Abuja. Ni dan majalisa ne na kasa, ba zan iya tserewa ba. Zan mika kai na ga 'yan sanda da zarar na dawo Abuja cikin mako mai zuwa. Babu wani laifin da na aikata," inji shi.

Legit.ng ta gano cewa Melaye ya zargi 'yan sanda da kin biyaya ga dokar kotu na mayar masa fasfo din fita kasashen waje. A cewarsa, kotu ta ce a bashi fasfo dinsa amma 'yan sanda sunki biyaya da umurnin.

"Yan sanda sun gurfanar da ni a kotuna 7. An bayar da umurin a mayar min da fasfo di na. Yanzu watanni biyar kenan amma 'yan sanda sunki biyaya ga umurnin kotun.

"Tun watan Afrilu an janye min masu tsaro na. Hukumar 'yan sanda sun ki mayar min da masu tsaron duk da cewa majalisa ta ce a mayar min. Hakan yasa ina fuskantar barazanar hari.

"Allah ne ya ke kiyaye ni. Ni bai mai laifi bane, zan kai kaina hedkwatan 'yan sanda da zarar na dawo a ranar Litinin 31 ga watan Disambar," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel