2019: Buhari ba zai iya magance kungiyar Boko Haram ba - CUPP

2019: Buhari ba zai iya magance kungiyar Boko Haram ba - CUPP

Hadakan jam'iyyun siyasa na Najeriya (CUPP) ta ce shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya cin galaba a kan mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram ba

A sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawun CUPP, Ikenga Imo Ugochinyere ya ce shugaban kasar ya rasa dabarun da zai yi amfani dashi domin yaki da 'yan ta'addan.

Ya ce Buhari ya fi mayar da hankali ne wajen lashe babban zaben shekarar 2019 a maimakon magance matsalar tsaron da ake fama da shi a arewa maso gabashin kasar.

2019: Buhari ba zai iya magance kungiyar Boko Haram ba - CUPP

2019: Buhari ba zai iya magance kungiyar Boko Haram ba - CUPP
Source: Twitter

DUBA WANNAN: APC ta mika sakon ta'aziyya ga PDP bisa rasuwar mambobinta da su kayi hatsarin mota

Ga wani bangare na sanarwar "CUPP tana damuwa saboda yadda shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da batun kallubalen tsaro da ake fama dashi a kasa, sai dai ya mayar da hankalinsa a kan batun yin tazarce duk da cewa bai tabuka komai ba."

"Menene yasa aka nada Janar Abdulrahman Dambazau a matsayin ministan harkokin cikin gda duk da cewa 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun kira direktan yakin neman zaben APC? Ta yaya Damnbazau zai banbance harkokin jam'iyyar APC da tsaron kasa? Wane irin gwamnati ne ke watsi da koke-koken al'ummarta."

"Nadin Dambazau ya nuna cewa dukkan fifikon da Sufeta Janar na 'yan sanda ke nunawa umurni ne daga shugaban kasa, ba muyi mamakin ganin shugaban kasar ne neman kara wa'addin Sufeta Janar din ba. Yanzu ya fito fili cewa shugaban kasa bai dauki harkar tsaro da muhimmanci ba."

"CUPP ta bukaci Janar Dambazau ya ajiye aikinsa a matsayin minister cikin gaggawa saboda a ceto rayuwar 'yan Najeriya wadda ke mutuwa saboda Buhari ya mayar da hankali kan siyasa yayin da mutane na mutuwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel