Sojin Najeriya sun baras da sabon yunkurin Boko Haram a Goniri, sun kwato manyan motocin igwa ta yaki

Sojin Najeriya sun baras da sabon yunkurin Boko Haram a Goniri, sun kwato manyan motocin igwa ta yaki

- Rundunar sojin Najeriya ta kashe yan Boko Haram a Goniri, karamar hukumar Gujba

- Yanzu haka yan garin na cikin murna don ko Dan ta'adda daya bai tsira ba

- Sojin sama sun taimaka wajen korar maharan Boko Haram

Sojin Najeriya sun baras da sabon yunkurin Boko Haram a Goniri, sun kwato manyan motocin igwa ta yaki

Sojin Najeriya sun baras da sabon yunkurin Boko Haram a Goniri, sun kwato manyan motocin igwa ta yaki
Source: Twitter

Rundunar sojin Najeriya ta kashe yan ta'addan Boko Haram a Goniri, karamar hukumar Gujba dake jihar Yobe. Rundunar sunyi wa yan ta'addan kaca kaca bayan da suka gano shirin harin da yan Boko Haram din zasu kai a ranar alhamis.

Yan ta'addan sun tsananta kai hare hare ga sojin a cikin kwanakin nan.

A ranar litinin ne yan ta'addan suka sha kan sojin a gurin zaman su dake Kukareta,kauye dake kilomita 20 zuwa Damaturu, jihar Yobe inda suka kashe sojoji 13 da dan sanda daya.

DUBA WANNAN: Titi Atiku ta farfado da ayyukanta na jin kai, WOTCLEF ta dawo kan aiki

A halin yanzu ana ta murna a Goniri don ba dan ta'addan da ya tsira. An kashe su,gawawwakin su da basu kirguwa suna nan zube a halin yanzu, Inji majiyar mu.

A wani cigaba da ya danganci hakan, sojin saman Najeriya sun bada bayanin yanda Operation Lafiya dole tare da sojin sama suka taimaka wajen korar yan Boko Haram a Baga.

Kungiyar yan ta'addan musuluncin nan mai suna ISWAP ce ta kai hari a garin masuntan da yammacin 26 ga watan Disamba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel