Bayan kashe masu yawon bude ido jiya, 'yan ta'adda sun gamu da fushin hukumar kasar Misra

Bayan kashe masu yawon bude ido jiya, 'yan ta'adda sun gamu da fushin hukumar kasar Misra

- A jiya ne suka saka bama-bamai a bas din

- Motar na dauke da masu yawon bude ido

- Yau sunsha ruwan wuta, 40 daga cikinsu sun mutu murus

- Yan sandar kasar Egypt sun kashe yan ta'adda da yawa

- A samamen da suka kai maboyar su sun kwaso makamai da ababen hada bam

- Tsaro ya tsananta a kasar musamman yanzu da ya zamo lokutan shakatawa

Bayan kashe masu yawon bude ido jiya, 'yan ta'adda sun gamu da fushin hukumar kasar Misra

Bayan kashe masu yawon bude ido jiya, 'yan ta'adda sun gamu da fushin hukumar kasar Misra
Source: UGC

Yan sandar kasar Egypt sun kashe yan ta'adda masu yawo yayin samamen da suka kai a maboyar su, inji ministan cikin gida.

Samamen yayi sanadin rasa rayukan yan ta'adda 40 a Giza da arewacin Sinai a safiyar litinin kamar yanda ma'aikatar ta fada.

Ma'aikatar tace yan ta'addan na yunkurin hare hare a wuraren shakatawa, majami'u da sojin kasar.

Samamen ya biyo bayan tashin bam a gefen titi a wata motar shakatawa a Giza. Babu kungiyar kuma da tace da sa hannun ta a tashin bam din wanda ya kashe masu yawon shakatawa uku na Vietnamese da mai jagorar su dan kasar Egypt daya.

Yan ta'addan sun so kai hari ne ga ma'aikatun tattalin arziki da na shakatawa da kuma majami'u, inji ma'aikatar tsaro

DUBA WANNAN: Ganduje na sauye-sauye a gwamnatinsa ana dab da gama zabe

Ta kara da cewa yan sanda sun kwace makamai da ababen hada bam.

Akwai tsaro mai tsanani a Egypt domin yanzu lokutan hutu ne da yawon bude ido.

Yawan shakatawa da baki ke zuwa kasar ya zamo wani jigo na tattalin arzikin kasar.

An samu kololuwar shi a 2010 da kasar ta samu sama da baki miliyan 14.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel