2019: Tsohon janar a rundunar soji ya shawarci masu takara da Buhari

2019: Tsohon janar a rundunar soji ya shawarci masu takara da Buhari

Tsohon gwamnan jihar Legas a mulkin soji, Birgideya janar Buba Marwa, ya ce babu gurbin zama shugaban kasa ga kowanne mutum bayan shugaba Buhari a shekarar 2019.

Marwa, shugaban kwamida zai bawa shugaban kasa shawara a kan dakile shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, ya fadi hakan ne yayin amsa tambayoyin 'yan jaridu a garin Yola, jihar Adamawa.

Marwa ya ce ba ya shakkar cewar shugaba Buhari zai sake lashe zabe a shekarar 2019.

"Kungiyar Buba Marwa ce ta fara shirya taron gangamin goyon bayan shugaba Buhari a 2016 domin yin godiya da nuna jin dadi bisa yadda shugaba Buhari ya yi kokari a bangaren inganta tattalin arziki, inganta tsaro da yaki da cin hanci.

"Zai kara lashe zabe a shekarar 2019 da yardar Allah," a kalaman Marwa.

Da yake magana a kan batun tsaro, Marwa ya jinjinawa sojojin Najeriya tare da yin kiran ga 'yan Najeriya da su goyon baya domin samun nasara a aiyukan su.

2019: Tsohon janar a rundunar soji ya shawarci masu takara da Buhari

Buba Marwa da Femi Adesina
Source: Depositphotos

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a kaddamar da wata manhaja ta musamman domin magance matsalar magudi a zabukan shekarar 2019.

Manhajar zata bawa 'yan Najeriya damar bayar da rahoton abinda ke faruwa a akwatunsu na zabe.

Sabuwar manhajar, da za a iya sakko da ita a wayar hannu daga shafin yanar gizo na INEC ko shafin sauke manhajoji na Google, zata iya bawa jami'an hukumar damar gano duk mazabar da aka sanar da samun wata matsala domin su gaggauta sanar da jami'an tsaron da zasu dauki matakin gaggawa.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da sunayen masu neman aiki a rukunin manyan ofisoshi

Dakta Mustapha Leeky, kwamishinan a hukumar zabe, ya bayyana cewar INEC ta bullo da manhajar ne domin dakile matsalar sayen kuri'u da aka fuskanta a zabukan jihohin Ekiti da Osun.

Ya ce, "mun kirkiri wata manhaja da bamu ji kafafen yada labarai na magana a kanta ba, a yanzu haka manhajar mai taken INEC i-reporter na nan a shafinmu na yanar gizo ko shafin sauke manhajoji na Google.

"Manhajar zata bawa 'yan Najeriya damar sanar da mu abinda ke faruwa a mazabunsu daga wayoyinsu na hannu ta hanyar aiko mana da hotuna kai tsaye. Mu kuma da mun samu sako zamu gano wacce mazaba ce kuma zamu dauki matakin da ya dace.

Kwamishinan ya kara da cewar sauke manhajar da amfani da ita kyauta ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel